1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawaye na kara samun galaba a rikicin Bangui

Usman ShehuJanuary 5, 2013

A Jamhuriyar Afirka ta tsakiya 'yan tawayen Seleka sun kara karbe iko da wasu birane, a wani abun koma baya ga sojan gwamnati.

https://p.dw.com/p/17Egb
Central African Republic President Francois Bozize (centre L, in blue) speaks to a crowd of supporters and anti-rebel protesters during an appeal for help, in Bangui December 27, 2012. Bozize on Thursday appealed for France and the United States to help push back rebels threatening his government and the capital, but Paris said its troops were only ready to protect French nationals. The exchanges came as regional African leaders tried to broker a ceasefire deal and as rebels said they had temporarily halted their advance on Bangui, the capital, to allow talks to take place. Picture taken December 27, 2012. REUTERS/Stringer (CENTRAL AFRICAN REPUBLIC - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Shugaba Francois Bozize da askarawansaHoto: Reuters

Yayin da ya rage 'yan kawanaki kalilan a gudanar da tattaunawa tsakanin gwamnatin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da 'yan tawayen Seleka da ke kokarin ganin shugaba Francois Bozize ya kau daga karagar mulki, mazauna garin Alinda sun ce 'yan tawaye Seleka sun karbe iko da gari a wannan Asabar.

Da ya ke zantawa da manema labarai game da wannan batu, wani mazaunin garin Bangassou da ke kusa da garin na Alinda Jean Balipio ya ce 'yan tawaye sun kutsa kai a garin ne a tsakar daren jiya Juma'a, ba tare da fuskanci turjiya daga dakarun gwamnatin ba, inda su ka karbe iko da birnin.

Kame wannan gari na Alinda wanda shi ne cikon na sha daya da 'yan tawayen su ka kame, kuma hakan ya sanya shakku ga zukatan al'ummar kasar da ma masu shiga tsakani a rikicin, dangane da fatan samun sararin warware takaddamar da ke tsakanin 'yan tawayen na Seleka da kuma shugaban kasar ta Jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

Mawallafi: Ahmed Salisu

Edita: Usman Shehu Usman