1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan tawaye sun karbi mahimman wurare a Yemen

September 21, 2014

Rahotanni daga birnin Sanaa, na cewa, 'yan tawayan kungiyar Ansaruallah na kasar sun karbe mahimman gine-ginen gwamnati

https://p.dw.com/p/1DGZm
Hoto: Reuters

Wuraran dai, sun hada da ofishin Firaministan kasar, da gidan talabijin na kasa da ke babban birnin, a cewar wasu manyan kusoshin gwamnatin kasar ta Yemen, inda a dai dai wannan lokaci kuma Firaministan kasar Mohamed Basindawa ya yi murabus daga mukaminsa, a wani mataki na nuna rashin amincewarsa da yanayin da shugaban kasar Abdrabuh Mansour Hadi, yake gudanar da mulkinsa, inda firaministan ke zargin sa da yin kane-kane kan komai.

'Yan tawayan 'yan Shi'a, sun kame mahimman barakokin soja da ke babban birnin wannan kasa, yayin da sojojin kasar suka yi kira da cewa kar a yi fada da 'yan tawayen. Hakan na zuwa ne kwana daya kacal bayan da aka sanar da batun rantaba hannu kan yarjejeniyar sulhu tsakanin bangarorin, bisa jagorancin manzo na musamman na Majalisar Dinkin Duniya Jamal Benomar da ya jagoranci tattaunawar.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Suleiman Babayo