1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan tawayen M23 ke iko da birnin Goma

Usman ShehuNovember 21, 2012

'Yan tawayen gabashin Kwango sun ƙwace iko da birni mafi girma a lardin gabacin ƙasar, wanda ke kewaye da ma'adinai

https://p.dw.com/p/16nWg
M23 rebels guard weapons given to them by the government's army in Goma November 21, 2012. Rebel forces in eastern Congo said on Wednesday they planned to take control of the whole of the vast central African country after they captured the eastern town of Goma while United Nations peacekeepers looked on. REUTERS/James Akena (DEMOCRATIC REPUBLIC OF CONGO - Tags: CIVIL UNREST)
Dakarun yan tawyen M23 cikin birnin GomaHoto: Reuters

Bayan watanni da aka yi yan tawayen ƙungiyar M23 suna barazanar kame babban birnin lardin gabashin jamduriyar demokradiyyar Kwango wato birnin Goma, daga ƙarshen dai sun cimma burinsu. Birnin Goma mai mazauna kimanin miliyan daya, kana yake da dubban sojojin MDD, karɓe iko da yan tawaye suka yi da birnin wani babban koma bayane ga gwamnati shugaba Joseph Kabila. Sanin irin mahimmancin da birnin Goma ke da shi, ya sa gwamnatin ta faɗa cikin ruɗani, don haka a fadin ƙasar ake ta yin zanga zanga.

epa03474001 Refugees flee the fighting between the rebel M23 forces and forces loyal to the government hear Goma, Eastern Congo DRC, 16 November 2012. A weeks-long ceasefire in the eastern Democratic Republic of Congo appeared to be breaking down 16 November amid reports of troop movements and ongoing fighting between government forces and rebels. Late on 15 November, the M23 rebel group said it had come under attack from government troops and retaliated. Congolese government officials, who say the rebels attacked first, indicated dozens have died in the latest outbreak of violence. Thousands of refugees have fled the massive central African country to neighbouring Rwanda over the past few days, adding to the hundreds of thousands already displaced. Kigali is accused by the UN and Kinshasa of backing the M23 movement, which is largely comprised of ethnic Tutsis, like the Rwandan government. EPA/Alain Wandimoyi
Yan gudun hijiran KwangoHoto: picture-alliance/dpa

Mazauna birnin Goma da ya kasance helkwatar gabashin Kwango, suna cikin yanyin da ya yi muni matuƙa. Inda kemanin mutane 500 mata da yara ƙanana suke fake a bayan buhunan yashi da sojojin MDD suka jibgi. Mutane na zaune a kan ƙasa babu tabarma balle bargo, ga shi kuma ana yin yayyafin ruwan sama. Ana kuma jin tashin bindodgi nan da can a ɗaukacin daren. Dan haka wannan dattijo da matarsa da yaransa shidda suka fake bayan buhunan yashi na sojan MDD, inda yake ganin aƙalla kasancewar sa kusa da sojan na MDD yana jin wuta da yaransa shine mafi alheri a gare shi, inda ya ƙara da cewa.

"Lamarin a gaskiya yana da wahalar juriwa. babu magani, babu abinci, muna matuƙar tsoron makomar ruyawar yayan mu, wadanda tun ranar Lahdin ta gabata ba su ci komai ba. Harsasai da rokokin da ake harbawa sun yi ta wucewa ta kawu nan mu. Kai ko da anan wajen dakarun MDD ma bamu tsira ba. Wadannan kwanaki duk mun yi su ne a sararin Allah ta a'ala. Kai yanayin akwai firgitarwa"

M23 rebels ride in a police truck in Goma November 21, 2012. Rebel forces in eastern Congo said on Wednesday they planned to take control of the whole of the vast central African country after they captured the eastern town of Goma while United Nations peacekeepers looked on. REUTERS/James Akena (DEMOCRATIC REPUBLIC OF CONGO - Tags: CIVIL UNREST POLITICS)
Dakarun M23 ke tuƙa motar yan sanda a cikin birnin GomaHoto: Reuters

A dai-dai lokacin da yan tawaye ke ta nausawa a bangaren da sojan gwamnati suke da iko. Har yanzu sai luguden wuta ake ji. Gabanin yan tawayen su kame birnin na Goma, sanda suka miƙa wa gwamnati buƙatar tattaunawa da kuma wa'adi na a yi hakan, amma shugaba Kabila yaƙiya. A lokacin kwamnadan yan tawayen M23 Innocent Kaina yace.

"Ya rage wa abokan gabanmu, idan sunce kuwa za su kai mana hari to za mu amshe iko da birnin Goma, domin muna da ƙarfin yin haka"

Daga ƙarshen dai bayan tsagaita wuta na watanni uku tsakanin sojan gwamnati da yan tawayen, barin wuta na kwanaki uku kacal ya sa yan tawaye M23 sun kame iko da birnin Goma.

REFILE - ADDING LOCATION WHERE PICTURE WAS TAKEN Displaced people cross the border from the Democratic Republic of Congo (DRC) into Rwanda, as seen from Gisenyi, November 20, 2012, as the Congolese Revolutionary Army fights with the DRC government army on the periphery of Goma, the capital of Congo's North Kivu province. Rwanda accused U.N.-backed Congolese forces of shelling its territory during a battle with rebels near the border on Monday but said it had no plans to respond militarily to what it called Kinshasa's "provocation". REUTERS/James Akena (RWANDA - Tags: CIVIL UNREST POLITICS) // eingestellt von se
Yan gudun hijran Kwango ke tsallakawa cikin ƙasar RuwandaHoto: Reuters

Gabanin yan tawayen su kame birnin dai, kusan jama'a sun shirya, inda tsaffi suka fara tserewa matasa masu ƙarfi a jika wasu suka tsaya gaban gidajensu, yayinda wasu suka laɓe bayan bangwaye. Don haka ma yan tawayen cikin sauƙi suka kame birnin domin, sojan gwamnati sun arce. Don haka suka tarar da wadanda ke gadin gidajensu kawai dake jiran abinda zai wakkana.

Mawallafa: Simone Schidwein/ Usman Shehu Usman

Edita: Mohammad Nasiru Awal

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani