1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yanayin 'yan gudun hijira ya tabarbare a Najeriya

Uwais Abubakar IdrisMarch 1, 2016

'Yan gudun hijira na yankin Arewa maso Gabashin Najeriya suna cikin tsaka mai wuya sakamakon karancin abinci da sauran abubuwan rayuwa da ake bukata.

https://p.dw.com/p/1I570
Nigeria Flüchtlinge in Maiduguri
Hoto: picture alliance/AP Photo

A Najeriya wahalhalun da ‘yan gudun ke fuskanta a sansanonisnu da ke Maiduguri helkwatar Jihar Borno inda suka fi yawa ta haifar da matsalolin na karancin abinci mai gina jiki da ta yi dalilin mutuwar yara kanana.

Sansanin ‘yan gudun hijira na Dallori da ke Maiduguri da ke zama mai girma, wanda a kiyasi yake da mutane dubu 26. A yanayi irin batun samun abinci kuma mai gina jiki muhimmi ne, wanda akasarin hakan kan haifar da matsala. Zara Musa na daya daga cikin ‘yan gudun hijira a sansanin na Dallori ta bayyana cewa:

Nigeria Boko Haram Anschlag
Sansanin 'yan gudun hijira a MaiduguriHoto: picture alliance/AP Photo/J. Ola

‘Eh to muna samun abincin amma dai ba isasshe ba ne muna dai lalabawa ana jaraba shi, kuma muna dan dinka hula mu samu kudin yaji da mai ba mu da komai sai dai a dafa dan garau-garau a ba mu, sai mu sayi mai da yaji mu zuba. A hakan ma ba za a baka ya isheka ba'

A farko dai bayanai sun nuna cewa yara 450 ne suka mutu a 2015 a sansanonin ‘yan gudun hijira 26 da ke Maiduguri, shin mene ne zahirin lamarin ne? Dr Sulaiman Mele shi ne darakta hukumar samar da lafiya matakin farko ta Jihar Borno:

‘Ainihin abin ba haka ba ne, wannan adadin na nuna duk yaran da suka rasu dalilin cututuka daban-daban. Amma yaran da suka mutu dalilin cutar tamowa ba su kaman 82 zuwa 83. Kuma wannan adadin ma na raguwa sosai, domin ana ba da magunguna na cutar ta tamowa ga yara'

bAmma ga Dr Franck Ndaie jami'in hukumar kula da lafiyar yara kanana ta Majalisar Dinkin Duniya da ke Maiduguri na mai bayyana abin da zai iya taimaka shawo kan matsalar:

Nigeria Befreite Geiseln Boko Haram
'Yan gudun hijiraHoto: picture-alliance/AP Photo/J. Ola

‘Kaman yadda nike fadi na dauki Maiduguri a matsayin babban sansanin ‘yan gudun hijira ne inda kayan da ake da su a yanzu kama daga abinci da asibitoci an kure su, don haka ake ririta su a tsakanin ‘yan gudun hijira da mutane da suke zaune. Zai fi kyau idan har aka samu kungiyoyin kasa da kasa su zo su taimaka. Ka san akwai mutane da sojoji ke cetowa suma suna bukatar a tallafa masu'

Bayanai sun nuna cewa kashi 10 ne na ‘yan gudun hijira da ke Jihar Borno ke a sansanonin inda saura ke rabe a gidajen 'yan uwa da abokan arziki, abin da ke nuna girma da sarkiyar wannan matsala da ke sanya nuna ‘yar yatsa ga mahukunta.