1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yancin shigi da fici na janyo cece-kuce tsakanin kasashen kungiyar EU

Umaru AliyuNovember 4, 2014

Birtaniya na adawa da 'yancin shigi da fici tsakanin kasashen Turai, abin da kungiyar ta ce ba mai tabawa, saboda alfanun da ya ke da shi ga ci-gaban kungiyar

https://p.dw.com/p/1Dgf7
NATO Gipfel in Wales 04.09.2014 Merkel mit Cameron und Rasmussen
Hoto: Reuters/Andrew Winning

A Ingila, muhawara game da yiwuwar ficewar kasar daga kungiyar hadin kan Turai tana kara tsananta, musamman yadda ake danganta wannan muhawara da batun yancin shigi da ficin jama'a a kungiyar ta hadin kan Turai. Jaridar Guardian ranar Litinin a shafinta na Intanet ta gabatar da wani rahoto game da wani jawabi da aka ce shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta yi, game da yiwuwar ficewar Ingila daga kungiyar. Wannan rahoto, inji jaridar ya dauki hankali matuka a Ingila.

Jaridar Guardian ita kanta ranar Lahadi ta rawaito cewar Merkel ta ce a shirye ta ke ta amince da ficewar Ingila daga kungiyar ta hadin kan Turai, muddin Ingila din ta nuna alamun ba za ta ci gaba da amincewa da yancin shigi da fici tsakanin al'ummar kungiyar ba. Jaridar Guardian, kamar sauran jaridu da dama a kasar ta Ingila, ta ambaci wani rahoto ne na mujallar labarai ta Jamus wato Spiegel.

A rahoton mujallar na ranar Litinin, ta nunar da cewar gwamnatin Jamus tana sa ran zai zama tilas Ingila ta janye daga kungiyar hadin kan Turai, idan har ta nemi tauye yancin shigi da fici a wannan kungiya. Mujallar Spiegel ta ambaci wata majiya wadda ta saurari tattaunawa a taron kolin baya-bayan nan tsakanin Angela Merkel da Pirayim minista David Cameron na Ingila.

Jean-Claude Juncker & Angela Merkel 18.10.2012
Jean-Claude Juncker na Tarayyar Turai da Angela MerkelHoto: picture-alliance/AP Photo

'Yancin shiga da fici tsakanin Turai na da mahimmanci

To sai dai jim kadan bayan haka, kakakin gwamnati a Berlin, yayi kokarin yin gyara ga abin da mujallar ta Spiegel ta ce ta ji, inda ya ce shugabar gwamnatin, a ganawarta da manema labarai lokacin taron kolin kungiyar hadin kan Turai ranar 24 ga watan Oktoba cewa tayi:

"Jamus ba za ta kyale wani ya nemi taba tsarin nan na yancin shigi da fici tsakanin kasashen kungiyar hadin kan Turai, wato EU ba. To amma hakan ba yana nufin wannan tsari ba ya tattare da matsaloli iri dabam dabam bane."

Cikin matsalolin da Merkel take magana kansu kuwa, har da yadda za a hana 'yan kasashen na kungiyar EU shiga wasu kasashenta domin karbar kudaden taimako da ba sa samu a kasashensu. Karar da Jamus ta kai gaban kotun kololuwa ta kasashen Turai yanzu haka tana jira a saurareta, inda ake sa ran kotun za ta yanke hukunci a watan Nuwamba.

EU Gipfel in Brüssel
Shugabannin TuraiHoto: Carl Court/Getty Images

David Cameron ya goyi bayan ficewa

A nashi bangaren, Pirayim ministan na Ingila, kamar yadda wani rahoto na jaridar Sunday Times ya nunar, ya ce matakin da kadai ya ke shirin dauka shi ne tilastawa yan kasashen Turai su fice daga Ingila, idan bayan watanni uku a kasar suka nuna alamun ba za su nemi yadda za su iya rike kai da kansu ba.

"Duk wani kokari da wani zai yi na gaban kansa domin yiwa shirin na yancin shigi da fici zagon kasa, a ganina, abu ne da ba zai dace da dokokin kungiyar hadin kan Turai ba. Mu a garemu, manufar nan ta daidaituwa tsakanin yan kasashen Turai abu ne mai muhimmanci kamar yadda yancin shigi da fici shima yake da muhimnci. Hakan kuwa ya shafi kayan ciniki da zuba jari da hidimomi da shigi da ficin jama'a."

Wannan fushi na Cameron ba ya samu ne saboda takaddamar shigi da ficin jama'a ba, amma sai saboda kudin da hukumar kungiyar hadin kan Turai tace Ingilan da sauran kasashen EU su biya a asusun wannan kungiya.