1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yanjin aikin direbobin jiragen kasa a Jamus

October 12, 2007
https://p.dw.com/p/Bu8b

Kungiyyar direbobin jiragen kasa na Jamus, sun shiga yajin aiki a yau.Yajin aikin da kungiyyar ta GDL ta fara, a yanzu haka ya kawo tsaiko ga zirga zirgar ma´aikata zuwa guraren aikin su.Yajin aikin na yau ya biyo bayan na share fage ne da suka yi mako daya daya gabata, wanda ya haifar da tsaiko ga al´amurran fasinjoji kusan miliyan goma.Kungiyyar direbobin dai na zargin cewa albashin su ba taka kara ya karya ba, idan aka kwatanta da takwarorin su na wasu kasashe a turai. A yanzu haka dai tattauna game da samo bakin zaren warware wannan matsala na nan na ci gaba da gudana.