1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yankin Kataloniya ya ayyana yancin kai

Abdullahi Tanko Bala
October 27, 2017

Dambarwar rikicin siyasar Spain ya dauki sabon salo, inda yankin Kataloniya ya ayyana yancin kai bayan da majalisar dattijan Spain ta umarci gwamnati ta gudanar da mulkin Kataloniyan kai tsaye daga Madrid.

https://p.dw.com/p/2mdJp
Spanien Barcelona - Befürwörter der Unabhängigkeit vor Katalanischem Regionalparlament
Hoto: Getty Images/Y. Herman

Majalisar dattijan Spain ta umarci gwamnatin Firaminista Mariano Rajoy ya karbi ragamar mulkin Kataloniya tare da gudanar da sha'anin mulkin yankin kai tsaye daga Madrid.

A yanzu dai Firaminista Rajoy zai gudanar da taron majalisar ministocinsa domin daukar matakin farko na gudanar da mulkin Kataloniya.

Sai dai kuma yan mintuna bayan matakin majalisar dattijan, yankin na Kataloniya ya sanar da ayyna 'yancin kai.

A zaman majalisar Kataloniya, yan majalisa 70 suka kada kuri'ar goyon bayan ballewa yayin da yan majalisa 10 suka kada kuri'ar rashin amincewa 2 kuma suka kasance yan baruwanmu.

Kawo yanzu dai babu wata kasa a duniya da ta goyi bayan ballewar yankin na Kataloniya.

A halin da ake ciki Firaministan Spain Mariano Rajoy ya bukaci jama'a su kwantar da hankula.