1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yansandan Kambodiya sun kona gonar wiwi

Abdul-raheem Hassan
July 19, 2017

Jami'an 'yansandan kambodiya sun kona shukar tabar wiwi har guda dubu 60,000, hukumomin sun ce sun bankawa gonar wuta ne bayan da yankin Takeo ya yi kaurin suna wajen noma ganyen tabar a fili karara.

https://p.dw.com/p/2goPH
Kolumbien Marihuana Cannabis
Hoto: Getty Images/AFP/R. Arboleda

Wannan dai shi ne karo na hudu a cikin shekaru biyu da jami'yan 'yansanda Kambodiya ke cillawa gonar wiwi wuta, ko da yake dai babu cikakkun bayanai da ke tabbatar da adadin asarar da kona tsirarran tabar wiwi da ya kai dubu 60,000, amma an yi kiyasin ana sai da rabin buhu kan kudi dalar Amirka 20.

Gwamnatin Kambodiya dai ta haramta noman tabar wiwi a dukkanin fadin kasar, amma wasu 'yan kasar na amfani da shi wajen girka abinci da zimmar magance wasu cututtuka, yayin da wasu ke sana'ar wiwi ga baki da ke ziyartar kasar yawon bude ido daga kakasashen ketere.