1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Buhari ya gana da Amina Ali

Gazali Abdou TasawaMay 19, 2016

Amina Ali da jaririyarta sun isa birnin Abuja fadar mulkin Najeriya a cikin wani jirgi da ya daukosu daga birnin Maiduguri tare da rakiyar mahaifiyarta mai suna Binta.

https://p.dw.com/p/1Iqr4
Nigeria Eine der durch Boko Haram verschleppten Schülerinnen ist frei
Hoto: picture-alliance/dpa/Nigerian Military

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana a wannan Alhamis da Amina Ali daya daga cikin 'yan matan sakandiren Chibok 219 da Boko Haram ta sace, wadda kuma aka yi nasarar ceto ta a ranar Talata 18 ga wannan wata na Mayu da muke ciki.

Yarinyar mai suna Amina Ali da jaririyarta sun isa birnin Abuja fadar gwamnatin Tarayyar Najeriya a cikin wani jirgi da ya daukosu daga birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno tare da rakiyar mahaifiyarta mai suna Binta.

Amina da mahaifiyar tata sun isa fadar shugaban kasa ta Aso Rock su duka fuskokinsu a lullube a karkashin jagorancin gwamnan jihar Borno Kashim Shettima da wasu mambobin gwamnati da mai bai wa shugaban kasar shawara kan harakokin tsaro da ministan tsaro na kasa da shugaban hafsan sojojin kasar. Shugaba Muhammadu Buhari dai ya sha alwashin Najeriya za ta tallafa mata a harakokin rayuwa da kuma na karantunta.