1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

yara kanana fiyr 500 suke gidajen yari na Cambodia

February 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuSj

Wani rahoton wata kungiyar kare hakkin bil adama a kasar Cambodia tace yara kanana 500 yan kasa da shekaru 18 suke tsare a gidajen yarin kasar,inda basa samun ababen more rayuwa baya ga muzguna masu da akeyi.

Rahoton yace wannan batu ya shafi yara 37 yan kasa da shekaru 6,da jarirai 22 dake zaune da uwayaensu a cikin gidajen yarin,inda basa samun isasshen abinci mai gina jiki da kuma samun ilmi,ko kula da lafiyarsu.

Hakazalika yara suna fuskantar barana ta musgunawa daga fursunonin da suka aikata miyagun laifuka.

Rahoton yace rashin tsabtaccen muhalli da magunguna da cunkoso sun kara ribanya yawan mace mace da ake samu a gidajen yarin na Cambodia .

Kasar ta Cambodia tana farfadowac ne daga shekaru na yakin basasa daya kare a 1998,inda yawancin cibiyoyin na kula da harkokin rayuwar jamaa da suka hada da gidajen yarin suka tabarbare.