1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yara masu aikin karfi a Ghana

August 27, 2014

Yankin Talensi da ke jihar sama ta gabas a kasar Ghana, yanki ne da yake da dinbin arzikin ma'adinai, amma kuma kananan yara ne ke aikin hakar ma'adinan

https://p.dw.com/p/1D2Ql
Kinderarbeit in Goldminen in Tansania
Hoto: HRW/Justin Purefoy

Wata kungiya mai zaman kanta da ke sanya idanu kan hakar ma'adinai mai suna Afrikids ta nunar da cewa kimanin yara 700 ne ta tabbatar da cewa suna wannan aikin na hakar ma'adinai a shekarar da ta gabata ta 2013 kadai a yankin Talensi.

A cewar dattawan yankin tun da ga shekarun 1990 ne dai masu hakar ma'adinan suke hako zinari a wannan yanki. Mafi yawan ma'aikatan kananan yara 'yan shekaru 10 dama 'yan kasa da haka. Atanga Akudugu yaro ne mai kimanin shekaru tara da haihuwa kuma wani dattijo ne ya dauke shi aikin hakar ma'adinai a wannan guri.

“Ina wannan aikin ne domin in samu abun da zan sa a cikina. Bamu da komai a gida. Ina so in daina saboda ina jin tsoron shiga cikin rami domin debo ma'adinan. Amma yanzu in na bari ba zan samu abun da zan ci ba."

Talauci ke sanya yara yin irin wadannan ayyukan

Richard Amoah ma'aikaci ne a wata kungiya mai zaman kanta ya kuma nunar da cewa kanan yara da dama na yin aiki a mahakar ma'adinai daban-daban. Ya ce yaran na yin aikin ne domin shine kadai hanyar da za su samu abun da za su sanya a bakin salati.

Kinderarbeit in Goldminen in Tansania
Hoto: HRW/Justin Purefoy

"Za ka samu yara kanana 'yan shekaru 11su suke ciyar da kakaninsu da kuma sauran kannaensu a gida kasancewar su basu da karfin da za su iya yin aikin. Dole ne yaran su fita domin samun abun da za su ciyar da su."

Dokokin kasar Ghana sun haramta bautar da kananan yara domin kuwa in har aka samu mutum da aikata wannan laifi za a ci tararsa 1000 na Cedin kasar ta Ghana, haka nan ma za a iya cin tarar iyayen yaron da suka amince ake bautar da shi din. An tanadi wadannan dokoki ne domin hana sanya kananan yara yin aiki a ma'adinai da ka iya cutar da rayuwarsu.

Babu aikin da yara basu yi wajen hakar ma'adinai

Yaran jihar sama ta gabas a kasar Ghana dai na yin ayyuka a dukkan matakan hakar ma'adinan. Matakin farko dai shine na debo duwatsu a karkashin kasa wanda nisan zurfin ramin hakara ma'adinan ka iya kaiwa mita 500. A cewar Richard Amoah akan daure yaron a zira shi cikin bokiti domin debo duwatsun da aka fasa. In sun shiga sai su loda duwatsuna buhu sannan a janyo shi su fito da su. A cewar Gordon Baba injiniyan hakar ma'adinai a kasar ta Ghana, za a iya samun mace mace a cikin ramin hakar ma'adinan.

Kinderarbeit in Goldminen in Tansania
Hoto: HRW/Justin Purefoy

“Ba kasafai akan samu irin wannan ba amman wasu lokutan ana iya samun tangarda a ramukan hakar ma'adinan misali idan gara ta cinye katakwayen da ake amfani da su a ramukan. Wani lokacin mutm guda ka iya haddasa mutuwar mutane masu yawa."

A shekara ta 2007 kungiyar ta Afrikids ta hada karfi da majalisar masarautar Talensi— Nabdam domin tserara da yaran daga wannan sana'a ta hanyar basu ihsani. Sai dai kawo yanzu kokarin da suke yi din ya ci tura kasancewar bai kawo wani sauyi ba kuma yaran na ci gaba da shiga cikin hadarurrukan da ke tattare da hakar ma'adinan.

Mawallafa: Maxwell Suuk/Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Pinado Abdu Waba