1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka: Kasuwanci mara shinge

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 12, 2019

Kasashen Afirka 54 sun amince da fara kasauwanci mara shinge a tsakaninsu. Kasashen Najeriya da Jamhuriyar Benin ne dai suka kasance na karshe cikin jerin kasashen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar.

https://p.dw.com/p/3LwB0
Warenverkehr an der Grenze zwischen Elfenbeinküste und Ghana
shige da fice na harkokin kasauwanci a Afirka ba tare da haraji baHoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

Yayin da kasashe 54 cikin 55 na kungiyar Tarayyar Afirka suka amince da yarjejeniyar kasuwanci mara shinge a tsakaninsu, masana da masu fashin baki da ma al'ummar nahiyar na ganin akwai gagarumin kalubale wajen fara amfani da yarjejeniyar, koda yake ana fatan samun gagarumin ci gaba da zarar an fara amfani da wannan yarjejeniya.