1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar Kwalambiya ta bar baya da kura

November 25, 2016

'Yan adawa Kwalambiya na mayar da martani kan sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma tsakanin ‘yan tawayen FARC da gwamnati da ke kokari kawo karshen sama da shekaru 50 na tashin hankali a kasar.

https://p.dw.com/p/2TFj5
Kolumbien Bogota Unterzeichnung Friedensvertrag
Hoto: Getty Images/AFP/L. Robayo

Matasa sun taru a birnin Bogota suna shewa da tafi da murna bayan da aka sake zaman sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin gwamnatin ta Kwalambiya da 'yan tawayen na FARC. Jim kadan dai bayan da Shugaba Manuel Santos na Kwalambiya  ya rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi wa kwaskwarima tsakanin gwamnati da ‘yan tawayen na FARC bisa jagorancin Rodrigo Londono.

A cewar ‘yan adawa dai kwaskwarimar ba ta taka kara ta karya ba kasancewar babu zancen daure ‘yan tawayen da suka aikata kisa da cin zarafi shekara da shekaru, ba a fayyace kan kadadrori da za su mallaka ba, an ce za su kebanta ne a kauyuka saboda ta'assar da suka tafka kawai. Hakan dai ya sanya rashin gamsuwa daga bangaren tsohon Shugaban kwalambiya  Alvaro Uribe da ke cewa matakin da aka dauka da ya biyo bayan kuri'ar raba gardamar ranar biyu ga watan Oktoba  da ta yi watsi da shirin zaman lafiyar bai dace ba. 

Kolumbien Ex-Präsident Alvaro Uribe Velez
Tsohon shugaba Alvaro Uribe na da ja kan yarjejeniyar zaman lafiyaHoto: picture-alliance/dpa/L.E. Noriega

Ya ce" Bana jin zai zama abu mara kyau idan na ce, wannan ba itacce hanyar da ta dace ba a rattaba hannu kan wannan yarjejeniya, akwai battutuwa masu muhimmanci da gwamnati ta ajiye gefe, za mu yi amfani da hakkin da ya rataya a wuyarmu na kare al'ummar Kwalambiya don kare hakkokin ‘yan kasa da gwamnati ba ta son magana a kansu idan mun je majalisa."

 

Banbancin ra'ayi kan yarjejeniyar zaman lafiya

A cewar Sanatan kuma jagoran adawa dai Uribe abin da ke faruwa yanzu ya sabawa alkawuran shugaba Santos da ya ci lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel. Ya ce "Hanyoyin da aka bi mun dauka cewa kamar yadda shugaban ya amince cewa za a martaba dimukaradiyya ne muna ganin wannan dai zai zama abin bakin ciki ga al'ummar Kwalambiya."

 

Da dama dai ‘yan kasar da suka fita gaban manyan allunan magiji inda aka nuna sa hannun kai tsaye sun nuna ra'ayoyinsu  mabanbanta:

Ya ce "Wannan rattaba hannu ba zai kawo zaman lafiya ba ne kawai  zai bude kofa ce ta zaman lafiya, sai kuma a zo a girka ginshiki mai kyau kan yadda zaman lafiyar zai dore."

"Wannan lokaci ne mai tarihi kamar lokacin 27 ga watan Satumba amma a yau ne hakikanin rattaba hannu kan zaman lafiya."

Kolumbien Historisches Friedensabkommen in Cartagena unterzeichnet
Kan 'yan Kwalambiya na rabe kan yarjejeniyar zaman lafiyaHoto: Reuters/J. Vizcaino

 

Babban abin da ke dagula hankulan wasu ‘yan adawar shi ne su na ganin akwai kullalliya cikin yarjejeniyar, da za ta share wa ‘yan tawayen na FARC hanya ta shugabanci a siyasance kamar yadda Sanata MARTA Lucia Ramirez, ke gani :

Ta ce T Tabbas an inganta yarjejeniyar sai dai abin da muke da ja a kai shi ne ta yaya za a budewa ‘yan tawayen kofa a siyasance nan da shekara guda su karbi jagoranci duk da irin ta'asar da suka tafka."

A mako mai zuwa ne dai 'yan majalisar kasar ta Kwalambiya za su tafka tasu muhawara kan wannan sabuwar yarjejeniya mai cike da cece- kuce da za ta nuna makomar kasar da ke da tarihin tawaye mafi dadewa a duniya da ya halaka mutane 260,000 miliyan bakwai aka rabasu da muhallansu tun bayan ballewar rikicin a shekarra 1964.