1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar tsagaita wuta a Siriya

Ahmed Salisu
December 30, 2016

An shiga rana ta farko bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin basasar Siriya da ke wakana tsakanin bangaren gwamnati da 'yan tawayen da ke kokarin hambarar da gwamnatin shugaban kasar Bashar al-Assad.

https://p.dw.com/p/2V2vi
Syrien Aleppo Waffenstillstand beschlossen
Hoto: picture-alliance/dpa

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce hankula sun kwanta a mafi akasarin yankunan kasar ko da dai an samu taho mu gama tsakanin wani bangare na 'yan tawaye da dakarun gwamnati a kusa da birnin Hama. A jiya ne dai shugaban Rasha Vladmir Putin ya sanar da wannan yarjejeniya da aka cimma wadda bangaren gwamnati da na 'yan tawaye suka yi na'am da ita amma kuma ya ce wannan batu bai shafi kungiyoyi masu dauke da makamai irin IS ba. Rikicin na Siriya da aka shafe fiye shekaru 4 ana gudanar da shi ya yi sanadin rasuwar dubban mutane da kuma jikkata wasu kana ya sanya miliyoyin 'yan kasar fantsama zuwa kasashen duniya da nufin neman mafaka.