1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan ta Kudu

Ahmed SalisuFebruary 2, 2015

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da madugun 'yan tawayen kasar Riek Machar sun sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniya ta zaman lafiya tsakanin gwamnati da 'yan tawaye.

https://p.dw.com/p/1EUFD
Salva Kiir und Riek Machar unterzeichnen Abkommen
Hoto: AFP/Getty Images

Masu shiga tsakani na kungiyar kasashen Afrika ta AU suka ce yarjejeniya ta fayyace irin hanyar da za a bi wajen samun zaman lafiya da kuma yadda bangarorin biyu za su yi rabon mukamai da zarar sun girka gwamnatin rikon kwarya inda Mr. Kiir zai cigaba da kasancewa shugaban kasa yayin da Machar zai zame masa mataimaki.

To sai dai duk da wannan 'yan tawayen sun ce dole ne a kara tsefe abubuwan da wannan yarjejeniya ta kunsa, inda Machar ya ce bangarorin biyu za su yi wani zama don tantance irin mukaman da kowa zai samu a ita wannan gwamnati da suke son ganin an samar.

A watan Janairun shekarar da ta gabata ma dai an kai ga cimma irin wannan yarjejeniya ta tsagaita wuta tsakanin gwamnati da 'yan tawayen na Sudan ta Kudu sai dai kafin tafiyar ta yi nisa bangarori biyun suka zargi juna da yin karen tsaye ga tanade-tanade yarjejeniyar.