1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsagaita wuta a Yemen

Suleiman Babayo
December 17, 2018

Za a fara aiki da yarjejeniyar tsakanin wuta tsakanin bangarorin da ke fada a Yemen kamar yadda wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar.

https://p.dw.com/p/3AGK7
Jemen Hafenstadt Hudaida
Hoto: Getty Images/AFP/S. Al-Obeidi

Wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar da cewa a wannan Talata za a fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta, domin kawo karshen rikicin da ke faruwa a garin Hodeida da kewaye na kasar Yemen. Haka sakamakon yarjejeniyar da aka kulla a kasar Sweden tsakanin gwamnatin Yemen da ke samun goyon bayan Saudiyya da kuma 'yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran.

Jami'in na Majalisar Dinkin duniya da ya yi magana da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP, ya bukaci a sakaye sunansa. A karshen mako mazauna garin na Hodeida da ke Yemen sun bayyana gwabza kazamin fada tsakanin bangarorin inda mutane da dama suka halaka.