1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar zaman lafiya a Kwalambiya

September 26, 2016

A wannan Litinin din ce ake sa ran sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin kungiyar 'yan tawayen FARC masu ra'ayin makisanci da gwamnati kasar Kwalambiya bayan tattaunawa ta kusan shekaru hudu.

https://p.dw.com/p/2Qa4l
Kolumbien FARC Friedensvertrag
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Duenas Castaneda

Wannan yarjejeniya dai za ta kawo karshen yakin da bangarorin biyu suka share shekaru 52 suna gwabzawa ba tare da wani bangare ya yi nasara ba. Kungiyar 'yan tawayen ta FARC dai ta share sama da mako daya ta na gudanar da babban taron Congres dinta wanda ya cimma matsaya a game da batun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar da gwamnatin kasar tare ma da nazarin yiwuwar canza kungiyar tawayen zuwa jam'iyyar siyasa. Bayan saka hannun kan yarjejeniyar tskanin bangarorin biyu, kasar Kwalambiyar za ta shirya zaben raba gardama kan batun ranar 2 ga watan Oktoba mai zuwa.