1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar zaman lafiya a Mali

Usman Shehu UsmanMarch 1, 2015

Bayan tsawon watanni takwas suna tabka mahawara, mahukuntan Bamako sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyoyin 'yan tawayen arewacin kasar

https://p.dw.com/p/1EMwa
Algerien Mali Friedensabkommen Unterzeichnung in Algier
Hoto: Farouk Batiche/AFP/Getty Images

Gwamnatin kasar ta Mali ta sa hannun zaman lafiya tsakaninta da wasu kungiyoyin mayakan arewacin kasar, to amma babbar kungiyar Abzinawa ta bukaci a bata lokaci, domin ta samu tuntubar magoya bayanta, talakawan yankin da suka kira Azawad. An dai wata takwas ana tattaunawar zaman lafiya, tsakanin gwamnatin Mali da 'yan tawayen arewacin kasar, wadanda suka nemi ballewa don kafa kasar kansu mai suna Azawad.