1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar zaman lafiya a Mali

Gazali AbdouMay 15, 2015

Wakilan 'yan tawayen Abzinawan Azawad sun kaurace wa taron rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta Bamako a ranar Juma'a.

https://p.dw.com/p/1FQTG
Algerien Mali Friedensabkommen Unterzeichnung in Algier Abdoulaye Diop
Hoto: Farouk Batiche/AFP/Getty Images

Wakillan kungiyoyi dabam-dabam wadanda ke da ruwa da tsaki cikin rikicin kasar ta Mali ne dai su ka hallara a babban zauran taro na Birnin Bamako a ranar juma'a da nufin sanya hannu akan takardar yarjejeniyar zaman lafiya da suka cimma a lokacin wani taro da suka gudanar a ranar Alhamis a birnin Alger .Sai dai ga bisa dukkan alamu tsugunne tashi ba ta kare ba a kasar ta Mali domin kuwa hadin gwiwar kungiyoyin 'yan tawayen Abzinawa yankin Azawad na CMA bai halarci zaman taron ba.

Da ma dai tun a gurin taron da ya gudana a birnin Alger wakillan 'yan tawayen abzinawan masu rajin samun kwaryakwaryar 'yancin cin gashin kai ga yankin na Azawad wadanda dama a bisa matsin lambar kasashen duniya ne suka halarci zaman taron suka ce ba zasu sanya hannu ba akan takardar yarjejeniyar a bisa hujjar cewa ba ta dauki wasu daga cikin jerin bukatunta ba. Sai dai duk da haka za a iya cewa hukumomin kasar ta Mali ba su yanke kauna ba tsakaninsu da 'yan tawayen yankin na Azawad.Abdullahi Diop shi ne Ministan kula da harakokin kasashen wajen kasar ta Mali:

Muhimmancin sanya hannu

Algerien Mali Friedensabkommen Unterzeichnung in Algier
Hoto: Farouk Batiche/AFP/Getty Images

"Lalle muna bukatar sanya hannu da gaggawa kuma muna fatan 'yan uwammu zasu fahimci cewa a yau abu mafi alkhairi garemu mu duka shi ne sanya hannu akan wanann yarjejeniya, dan mu samu a nan gaba mu ga matakkan da suka dace mu dauka domin maido da kwanciyar hankali da ma zartar da alkawurran da mu ka dauka a cikin wanann yarjejeniya".

Sai dai daga nata bangare kungiyar "yan tawayen Plate Forme ta kasar ta Mali da ke goyan bayan manufofin hukumomin Bamako da ma shirin sasantawar sun halarci wanann zama. Ibrahim Diallo daya daga cikin jagororin wanann kungiya ya yi karin bayani a game da dalillansu na bada hadin kai ga shirin:

Matsuwa da maido da zaman lafiya

" 'Yan Mali sun kosa da wanann lamari dan haka muma kamar sauran 'yan Malin mun matsu mu ga zaman lafiya ya dawo a cikin kasarmu. musamman ni dan asalin yankin arewacin kasar, na san irin yadda al'ummarmu ta tagayyara dan haka na matsu in ga an kawo karshen wanann matsala domin suma su wala da yin kai da kawo a cikin kasarsu iya son ransu".

Algerien Mali Friedensabkommen Unterzeichnung in Algier Bilal Acherif
Hoto: Farouk Batiche/AFP/Getty Images

Yanzu haka dai kungiyar tarayyar Turai wacce ke da hannu a cikin shirin sasantawar 'yan kasar ta Mali ta yi kira ga bangarorin kasar da ba su halarci taron na birnin Bamako ba da su zo su saka hannu koda daga bayan taron ne. Kana ta sha alwashin sanya ido akan ganin dukkannin bangarorin sun mutunta matsayar da aka cimma.

A shekara ta 2012 ne dai kungiyoyin 'yan jihadi da na 'yan tawayen abzinawa su ka mamaye yankin arewacin kasar ta Mali kafin daga bisani kasashen duniya su kwato shi da karfin soja a shekara ta 2013. Saidai har yanzu yankin arewacin kasar ta Mali ya kasa komawa a karkashin ikon gwamnatin Bamako, yankin da ke ci gaba da kasance a hannu tsageru da kuma kungiyoyin 'yan tawayen abzinawa masu rajin ballewar yankin Azawad daga hadaddiyar kasar ta Mali.