1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar zaman lafiya a Mozambik

January 4, 2017

'Yan tawayen kasar Mozambik sun ba da sanarwar tsawaita yarjejeniyar zaman lafiya da suka cimma da gwamnatin kasar.

https://p.dw.com/p/2VGBA
Mosambik Soldaten Symbolbild
Hoto: Getty Images/AFP/M. C. Mac' Arthur

Tsawaitar yarjejeniya zaman lafiyan da aka yi tsakanin kungiyar RENAMO da gwamnatin Mozambik dai ta sanya fata a zukantan 'yan kasar da ma wanda ke rike da madafun iko na samun zaman lafiya mai dorewa da kuma kawo karshen zub da jini musamman irin wanda aka gani a shekarar da ta gabata. Shugaban kungiyar ta RENAMO Afonso Dhlakama ya ce sun yanke wannan hukunci ne da nufin samun wani yanayi na ci gaba da zantawa da hukumomi don wanzar da zaman lafiya yalwa:

'' Kara wa'adin yarjejeniya da muka yi da kwanaki sittin zai ba da dama ta samun sukunin ci gaba da tattaunawa da mahukunta a Maputo cikin ruwan sanyi ga dukannin bangarorin biyu wato RENAMO da kuma gwamnati.'' 

Mosambik Soldaten bei einer Parade in Maputo
Hoto: imago/Xinhua

Mr Dhlakama ya ce duk da cewar an samu tashin-tashina a wasu wuraren amma dai a jimlace za a iya cewar lamura na tafiya yadda suke so tun bayan da suka ba da sanarwa ta tsawaita yarjejeniyar wadda aka yi a ranar Takatar da ta gabata, lamarin da ya sanya ya ce ya na tunanin wannan hukunci da suka yanke zai haifar da da mai idanu. To sai dai a daura da wannan, Armindo Chavana da ke yin sharhi kan lamuran yau da kullum a kasar Mozambik na ganin ya kyautu a ce an kai ga cimma yarjejeniya ta dindindin don kawo karshen takun sakar da ke akwai tsakanin bangarorin biyu maimakon a rika kara wa'adin yarjejeniya daga lokaci zuwa lokaci.