1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Mohammad Nasiru Awal AH
February 8, 2019

Jagororin kungiyoyi masu daukar makami 14 da shugaban kasa Faustin-Archange sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya a Khartoum babban birnin Sudan karo na 12 ake cimma yarjejeniya a kasar.

https://p.dw.com/p/3D0TE
Zentralafrikanische Republik Präsident und Rebellen unterzeichnen Friedensabkommen in Bangui
Wannan wani tsohon hoto ne, na tattaunawar zaman lafiyar da aka yi a birnin Bangui na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a shekara ta 2012Hoto: Getty Images/AFP/F. Vergnes

 Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda ta leka kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya tana mai tambaya "Zaman Lafiya a Afitka Tsakiya?" Sannan sai ta ci gaba kamar haka: Jagororin kungiyoyi masu daukar makami 14 da shugaban kasa Faustin-Archange sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya a Khartoum babban birnin kasar Sudan. Ta ce wannan ita ce ta bakwai da aka sanya wa hannu tun a shekarar 2012, dukkan yarjeniyoyin wanzar da zaman lafiyar sun ruguje. An dai bayyana sabuwar yarjejeniyar da cewa za ta bude sabon babi ga kasar ta Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da ma al'ummarta, za ta kuma zama matakin sansanta 'yan kasar, wanda zai samar da yanayi na kwanciyar hankali da ci-gaban kasa. Ko da yake ba a yi bayani dalla-dalla abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa ba, amma muhimmi n batu a tattaunawar shi ne bukatar 'yan tawaye na a yi musu afuwa, abin da kawo yanzu gwamnatim ta ki.


Sau 12 ana cimma yarjejejiyar zaman lafiya  tsakanin bangarorin da ke gaba da juna a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Zentralafrikanische Republik | Naturschutz in Krisengebieten | Soldaten vor dem Präsidentenpalast in Bangui
Hoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

Matsalar cin hancin da rashawa a Afirka ta Kudu ta wuce yadda ake zato inji jaridar Neue Zürcher Zeitung. Jaridar ta ce kawo yanzu badakalar da ta shafi kamfanin iyalin Gupta ta kasance a tsakiyar duk batutuwan cin hancin da rashawa a Afirka ta Kudu. Amma yanzu ya fito fili cewa matsalar ta cin hanci ta samu gindin zama a bangarori da dama na hukumomin gwamnati ciki har da na asusun tara kudin fansho. Sai kuma kamfanin Bosasa na wani farar fata Afirka ta Kudu wato Angelo Agrizzi wanda ya yi ta fasa kwai a kwanakin nan. Shi dai Agrizzi ya ce kamfaninsa ya kwashe shekaru yana ba wa hukumomi hanci don samun kwangila da sau tari ba ya yin aikin tsakani da Allah. Yana kuma ba wa lauyoyin gwamnati hanci don kada a bincikeshi. Jaridar ta ce wannan abin kaico ne kasancewa shugaban kasa Cyril Ramaphosa ya yi alkawarin gudanar da bincike tun bayan darewarsa kan kujerar shugabankasa a watan Fabarairun 2018 an kuma kafa kwamitocin bincike da dama amma har yanzu ba wanda ya gurfana gaban kotu.

Rasha na kokarin sake komawa cikin kassahen Afirka domin kaddamar da ayyuka musammun ma a kan batun hako  ma'adinai

Äthiopien Addis Abeba Sergei Lawrow und Moussa Faki
Ministan harkokin waje na Rasha Serge Lavrov tare da Moussa Faki shugaban kwamitin kungiyar tarrayar Afirka AUHoto: Getty Images/AFP/Z. Abubeker

Rasha ta koma Afirka a cewar jaridar Berliner Zeitung tana mai cewa gwamnatin Mosko ta sake gano muhimmancin nahiyar Afirka a siyasance inda yanzu haka take neman sabbin hanyoyin samun albarkatun karkashin kasa na Afirka, tana kuma neman sabbin kawaye a nahiyar. Jaridar ta ce Rasha na gudanar da manyan ayyuka a sassa dabam-dabam na Afirka, tana kuma tura sojojinta a matsayin masu horas da sojojin wasu kasashen Afirka. Ita ma kasar Rasha tana bin irin manufar kasar Sin na kin tsoma bakinta a harkokin cikin gidan kasashen Afirka, abin da ke kama da goyon bayan gwamnatocin mulkin kama karya.