1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawaitar zubar da jinin fararen hula a Najeriya

Mohammad AwalSeptember 30, 2013

A yayin da Najeriya ke shirin cika shekaru 53 da samun 'yancin kai, mutane da dama ne aka hallaka a karshen mako, a wasu jerin hare-haren da aka kai a sassa daban-daban na arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/19rvm
Hoto: Getty Images/AFP

Kashe-kashen jama'a da aka fuskanta a karshen mako a Najeriya, inda fiye da mutane 100 suka mutu sakamakon hare- haren da 'yan bindiga suka kai a sassa daban –daban na kasar, ya haifar da maida martani da ma tsoron kara tabarbarewar da yanayin tsaron kasar ke yi, a dai dai lokacin da Najeriyar ke cika shekaru 53 da samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka. Karuwar kai hare-haren da suka yi dalilin mutuwar mutanen da har yanzu ake ci gaba da neman sanin zahirin adadinsu ya faro ne daga jihar Yobe inda aka harbe yara 'yan makaranta sama da 50, ya zuwa ga jihar Kaduna da ‘yan bindiga suka hallaka wasu mutane 15, labarin dai duka daya ne a jiyar Benue inda can ma rikici ne tsakanin fulani da 'yan kabilar Tibi wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 33.

Irin yadda hutun karshen makon ya kasancewa 'yan Najeriya cikin tashin hankali da juyayin inda aka dosa a kasar kenan, domin koda a Abuja karshen makon ya kasance wanda aka fuskanci fashi da makami a unguwanin da ake wa kalon suna tudun mun tsira, irin na Apo da Gwaraimpa, duka wannan na faruwa ne a dai dai lokacin da Najeriyar ke jajiberin bikin cikarta shekaru 53 da samun 'yancin kanta. Wannan ya sanya tambayar hadarin da wannan hali ke tattare da shi da ma inda aka dosa. Malam Sani Aliyu shine Daraktan Gudanarwa na kungiyar wanzar da zaman lafiya da tsaro da kare 'yancin dimokradiya da ke Abuja.

Nigeria Angriffe von Extremisten
Ginin wata ma'aikata a jihar Kaduna da aka kai harin bama-bamai a karshen mako.Hoto: picture-alliance/dpa

‘'Gaskiya a kwai hadari sosai, domin ko ina ka shiga yanzu a kwai wannan batu na kashe-kashe banda sata da fashi da makami, ga 'yan taratsi don haka muke jan hankalin shugaban Najeriya Jonathan ya dauki mataki, domin kudaden da suke fitarwa da sunan tsaro, amma kuma bama ganin komai, har yanzu ba'a ga tasirinsu ba don haka ba zama za su yi, su yi barci ba, saboda kasar ba lafiya''.

Ya ya makomar Najeriya za ta kasance?

Karuwar kai hare-hare da zub da jinin bayin Allah sakamakon sukurkucewar al'amuran tsaro dai, na zama babban kalubale ga makomar Najeriyar da ke fuskantar zabe nan da shekara ta 2015, wanda duk da cewa sauran kusan shekaru biyu a kai gareshi ana ta fuskantar karuwar zaman tankiya a tsakanin al'umma. Duk da cewa yanayin da ake ciki na jefa tsoro ga zukatan 'yan Najeriya, amma ga Malam Nasiru Zaharaddeen mai taimakawa shugaban Najeriya na musamman a fannin harkokin yau da kullum yace, nasarorin da suke ganin ana samu ya kamata su kwantar da hankulan jama'a.

‘'Abubuwan da aka yi, a gaskiya dokar ta bacin nan ta kwantar da yawancin hare-haren da ake kaiwa gaba gadi, yanzu sai dai su buya su yi, wanda shima in Allah ya yarda da hadin kan jama'a ana samun sauki, domin hadin kan na cikin abubuwan da yake taimakawa sosai. Domin an san inda suke an matse su an tura su an hana su sakat. Najeriya kasa ce mai tasowa kuma muna ci gaba da tasowa abubuwan za su kara gyaruwa, sai dai fatan Allah kawo wannan gyara cikin lokaci''.

Nigeria Soldaten
Sojojin Najeriya na Rangadi.Hoto: Quentin Leboucher/AFP/Getty Images

Amma ga Hounarable Baba Kaita na majalisar wakilan Najeriya, ya na ganin lokacin boye-boye a game da batun halin da yanayin tsaron Najeriyar ya shiga fa ya wuce, a kwai bukatar shaidawa juna gaskiya, ko menene dalilinsa.

'Yan Najeriya sun gaji da gafara Sa

‘'To ai gaskiya batun harkara tsaro a Najeriya babu ita kwata-kwata, domin idan ka dauki yammacin kasar nan barayi da rana suke shiga bankuna da gidaje su yi satarsu, a arewa kuma ga wadannan kashe-kashe da ake ta yi, sannan sojoji na ta yada jita-jita ta shirme kawai . Mecece jita-jita ta banza yau su ce sun yi kaza amma kuma kaji ana ci gaba da kai hare-haren''.

Duk da cewa mutane kan fara sabon mako cike da fata da annuri a zukatansu, to amma ga 'yan Najeriya da dama, hare-haren da aka kai a karshen makon na zama lamarin da ya jefasu cikin juyayi da hanzarin neman mafita daga wannan matsala dake zama ci gaban mai hakan rijiya.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Lateefa Mustapha Ja'afar/MAB