1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawan adadin mutane da suka mutu a ƙasar Jamaika ya ƙaru

May 26, 2010

Gwamnatin ƙasar Jamaika ta ƙudiri aniyar ci-gaba da farautar 'yan bindiga du da irin ƙaruwa yawan mutane da suka mutu a faɗan da yan sanda ke yi da 'yan bindiga

https://p.dw.com/p/NY2S
Hoto: AP

Yawan adadin mutanen da suka mutu a ƙasar Jamaika a faɗan da 'yan sanda suke yi da wasu 'yan bindiga daɗi ya haura daga mutun 31 zuwa 49.

Jami'an tsaro waɗanda suka kwashe kwanaki fuɗu suna karawa da 'yan bindiga a fafutukar ta neman sa hannu akan wani shugaban wata ƙungiyar masu safarar miyagun ƙwayoyi Christopher Dudus, wanda Amirka ke nemansa ruwa jallo, sun shaida cewa fararar fula 39 suka mutu da kuma 'yan sanda uku.

Amerikan dai na neman a miƙa mata Christopher ɗin domin ya fuskanci hukumci bayan zargin da ake yi masa da hannu a kashe kashen gilla da aka samu kusan ɗari tun a shekara ta 1980 akan zancen mafiyar ta cinikin ƙwaya .

Mawallafi :Abdourahamane Hassane

Edita : Ahmad Tijani Lawal