1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawan wadanda suka rasa rayukansu a hadarinjirgin Najeriya ya karu

December 12, 2005
https://p.dw.com/p/BvGt

A Najeriya, yawan mutane da suka rasa rayukansu a cikin hadarin jirgin sama a birnin Port Harcourt, ya karu, yayinda mutane 4 daga cikin 7 da suka tsira da ransu cikin hadarin jirgin Saman suka rasu a asibiti, sakamakon raunuka da suka ji a lokacin hadarin.

Jirgin na kanfanin Solsoliso ya taso ne daga Abuja zuwa birnin PortHarcourt yayinda ya kama wuta a lokacinda ya sauka.

Wannan shine hadarin jirgin sama na biyu a Najeriya cikin watanni 2 wadda yayi sanadiyar rayukan mutane da dama.