1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawan 'yan gudun hijira ya karu a duniya

May 14, 2014

Babbar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duiya ta ce wannan adadin shi ne mafi yawa tun bayan yakin duniya na biyu.

https://p.dw.com/p/1Bzdo
Jordanien, Flüchtlingslager Saatari Ausschreitungen UNHCR 06.04.2014
Hoto: Reuters

Yawan mutanen da ke tsere wa rikice rikice na daukar makami da ayyukan tarzoma ya kai wani mizani da ba a taba ganin irinsa ba tun lokacin yakin duniya na biyu. Majalisar Dinkin Duniya ta ce a bara mutane miliyan 33 da suka hada da kananan yara da mata da kuma maza suka kasance 'yan gudun hijira a cikin kasashensu na asali. Wannan ya haura yawan na bara waccan wato shekarar 2012, da kimanin mutane miliyan hudu da rabi, inji babbar hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Geneva. Hukumar ta ce a kan dauki tsawon shekaru 17 kafin 'yan gudun hijirar na cikin gida su koma yankunansu na asali. Ta ce rikicin kasar Siriya na daga cikin dalilan karuwar yawan 'yan gudun hijirar. A wani labarin kuma yawan bakin haure da ke shigowa Turai ta barauniyar hanya ya karu inji hukuma ta 'yan guduin hijira. A watanni hudun farko na wannan shekara 'yan gudun hijira fiye dubu 400 ne aka tsare a kan iyakokin kasashen tarayyar Turai.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman