1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaya manufofin Afirka zasu kasance bayan zaben Jamus?

September 24, 2013

Masu rajin ganin an kyautatawa nahiyar Afirka cikin gwamnatin Jamus suna fatan sabuwar gwamnatin kasar zata bullo da sabbin manufofi kan nahiyar

https://p.dw.com/p/19nRG
Mali's interim President Dioncounda Traore (L) shakes hands with Germany's Minister of Economic Cooperation and Development Dirk Niebel (R) during their meeting in Bamako on March 23, 2013. Niebel called for Mali's authorities to hold as planned elections in July, a condition for the full recovery of German help in the African country in crisis for a year. AFP PHOTO / HABIBOU KOUYATE (Photo credit should read HABIBOU KOUYATE/AFP/Getty Images)
Hoto: Habibou Kouyate/AFP/Getty Images

A yayin da jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta lashe zaben majalisar dokokin kasar da ya gudana a ranar Lahadin da ta gabata, masu rajin ganin an kyautatawa nahiyar Afirka da ke cikin gwamnatin Jamus, sun bayyana fatan sabuwar gwamnatin da za a kafa, za ta bullo da sabbin manufofin da za su kara mutunta nahiyar, da kuma nuna goyon baya ga harkokin kasauwancin da Jamus ke yi a Afirka.

Dama dai ana samun kyautatuwar huldar da ke tsakanin Jamus da nahiyar Afirka, musamman bisa la'akari da cewar, bayan kama aiki a matsayin ministan kula da harkokin raya kasashe a Jamus a watan Janairun shekara ta 2010, Dirk Niebel, ya fara rangadinsa na farko zuwa Afirka ne ana kasa da watanni shida da kama aiki, kuma ya bayyana irin abin da ya gano a lokacin:

Ya ce " Na fahimci cewar kalubale na zuwa ne da matsaloli a nahiyar Afirka, kuma suna bukatar yi namijin kokari domin tinkararsu. Saboda haka ne gwamnatin tarayyar Jamus ta bada fifiko ga hakan a dangantakarta da nahiyar Afirka ta fannin raya kasa."

Sakamakon hubbasar da ma'aikatar raya kasashe ta Jamus ta yi a karkashin minista Dirk Niebel dai, an sami ci gaba mai ma'ana a irin manufofin Jamus ga nahiyar ta afirka, kamar yadda wasu kungiyoyi ke fadi. Nicola Röschert, shugaban kungiyar AfricaAvenir da ke da rajin kyautata makomar Afirka, wadda cibiyarta ke a birnin Berlin na Jamus, kana take taka rawa a harkokin bunkasa Ilimi a nahiyar Afirka, ya ce akwai bukatar duk wata sabuwar gwamnatin da za a samar a Jamus, bayan zabukan, ta koyi darasi daga irin abubuwan ci gaban da aka samu a baya bayannan, tare da rungumar dabi'ar tattaunawa da su kansu 'yan Afirka cikin ayyukan raya yankunansu:

Entwicklungsprojekte aus Deutschland
Aiyukan taimakon raya kasa a AfirkaHoto: Deutsche Botshaft Pristina

Ya ce " Abu mafi muhimmancin da 'yan Afirka ke begen samu shi ne damawa dasu. Mu a kungiyar AfrcaAvenir, muna bunkasa batun tattaunawa da su kansu 'yan Afirka, kuma ko da shike muna da hanyar yin haka ta ma'aikatar kula da harkokin tattalin arziki da raya kasashe, amma akwai ayar tambaya a kan ko me ya sa gwamnatin tarayya ba ta yin amfani da damar wajen gayyato su 'yan Afirka domin ganawa da su a kan ta yaya za su tattauna da su ido na ganin ido."

Duk da cewar, akwai wadanda ke hubbasa wajen taka rawa a harkokin kasuwanci daga nahiyar Afirka, amma sau da dama, rashin samun daidaito a farashin hajojin da suke kaiwa kasuwannin duniya ne ke janyo musu cikas ga irin namijin kokarin da suke yi wajen bunkasa tattalin arzikinsu, wanda ke faruwa sakamakon irin tallafin da gwamnatocin kasashen da suka ci gaba ke baiwa alal misali manomansu, wanda kuma ke kawo koma baya ga irin farashin kayayyakin da manoma a nahiyar Afirka ke samarwa. Uschi Eid, mataimakiyar shugabar gidauiniyar hadin gwiwa a tsakanin Jamus da Afirka, kana tsohuwar wakiliyar tsohon shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schröder game da harkokin da suka shafi nahiyar Afirka a kungiyar kasashen da ke da karfin tattalin arziki ta G8, ta ce ci gaban da ake batu, bai taimakawa Afirka sosai:

Ta ce " Afirka ba ta samun gajiyar da ta dace a irin kawancen da take yi a kasauwannin duniya. A kullum kira nake yi ga tsara manufofin harkokin wajen Jamus ta yadda za su taimakawa makwabtanmu. Tunda muna yin aiki domin warware matsalolin da ke addabarmu, kamata yayi mu binciko hanyoyin da za mu hada kai, mu shawo kan matsalolin."

Bildergalerie Deutscher Entwicklungstag in Bonn
Hada kai domin taimakawa AfirkaHoto: DW

Wani batu kuma shi ne tallafawa Afirka shawo kan matsalolin siyasar da ke addabarta cikin shekaru da dama.

Mawallafi: Duckstein/Saleh Umar Saleh
Edita: Umaru Aliyu