1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yiwuwar zagaye na biyu na zaben Tunisiya

Ahmed SalisuNovember 24, 2014

Rahotani na nuna cewar akwai alamun zuwa zagaye na biyu na zaben shugabar kasar Tunisiya wanda shi ne irinsa na farko tun bayan da aka yi juyin juya hali.

https://p.dw.com/p/1DsE3
Wahlen in Tunesien
Hoto: picture alliance/abaca/F. Nicolas

Masu aiko da rahotanni suka ce daga irin sakamakon da ake samu ko da dai ba na hukuma ba ne na nuna cewar tsohon firaministan kasar Beji Caid Essibsi na jam'iyyar Nidaa Tounes yanzu haka na da kashi 42.7 cikin 100 na kuri'un da aka kada yayin da abokin hamayyarsa kana shagaban kasar mai rikon kwarya Moncef Marzouki ke da kashi 32.6.

Idan dai har sakamakon ya cigaba da kasancewa a haka, to za a kai ga yin zagaye na biyu na zaben wanda ake sa ran gudanar da shi cikin watan Disamban da ke tafe ko da dai ba a kai ga sanya rana ba.