1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Farfado da shirin zaman lafiya a gabas ta tsakiya

Abdullahi Tanko BalaNovember 10, 2009

Kudirin Obama na ƙulla sabuwar dangantaka da ƙasashen larabawa da ma duniyar musulmi.

https://p.dw.com/p/KTE0
Shugaba Barack Obama yayin da yake jawabi a MasarHoto: AP

Watanni goma bayan da Barack Obama ya hau karagar mulki kuma bayan tsawon kai komo na shiga tsakani da wakilinsa na musamman a gabas ta tsakiya George Mitchell yayi ta yi a yankin, har yanzu babu wani abin azo a gani da aka cimma. Robert Malley daraktan shiyyar gabas ta tsakiya na cibiyar nazari da sasanta rikice rikice yace ya kamata gwamnatin Amirka ta sake duba matsayin shirin samar da zaman lafiyar.

" A kowane hali dai, tilas ne gwamnati ta fuskanci gaskiyar cewa a dukkan yunƙurin da take yi na kyautata yanayin zamantakewa da kuma aiki kan halin da ake ciki, akwai buƙatar ta san cewa tazarar da ake da ita a yau tafi ta jiya ta jiya kuma giɓinta ya kai yadda ba zaá iya cikewa cikin sauƙi ba".

Babu dai wani tasiri da sabuwar dabarar ta haifar. Ana kuma iya ganin haka musamman ga aikin faɗaɗa matsugunai da Israila ke yi wanda haramtacce ne a ƙarƙashin tsarin dokokin ƙasa da ƙasa. Da farko Obama yayi kira ga Israila ta dakatar da waɗannan gine gine. Sai dai kuma yayin da Israila ta baiyana ƙin amincewa da wannan buƙata sai Amirka ta ja da baya kan batun. Ƙasashen Musulmi sun maida martani da matuƙar mamaki. Akan haka ne sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ta yi bayani tana mai cewa ga alama an yiwa matsayin Amirkan saɓanin fahimta game da dakatar da faɗaɗa matsugunan na Yahudawa. " Matsayinmu kan matsugunan bai sauya ba, ina so na maimaita cewa matsayin mu akan matsugunai bai sauya. Bamu amince da halascin ayyukan faɗaɗa matsgunai ba. Abinda muka samu daga Israila shine dakatar da faɗaɗa sabbin matsugunai da kawo ƙarshen share wuri zauna, haka zalika babu wani izinin gini da zaá lamunta da shi.

Wannan dai ya tunato da ɓacin rai ga Falasɗinawa. A lokacin taron Camp David tsakanin marigayi shugaban Falasɗinawa Yasser Arafat da tsohon Firaministan Israila Ehud Barak a watan Yuli na shekara ta 2000 yunƙurin ya gaza cimma nasara wanda kuma aka ɗora alhakinsa akan Yasser Arafat.

Robert Malley daraktan shiyyar gabas ta tsakiya na cibiyar nazari da sasanta rikice rikice wanda ya kasance a wajen wannan taro yace Arafat ya ƙi amincewa da tayin da Ehud Barak ya gabatar masa wanda baá taɓa samun irinsa ba, alhali kuma shi bai gabatar da wani tayi madadinsa ba.

Tun dai daga wannan lokaci ne dangantakar Amirka da Falasɗinawa ta riƙa samun koma baya, har zuwa bayan rasuwar Yasser Arafat. An sami ɗan kyautatuwar dangantaka ne a lokacin da Mahmoud Abbas ya karɓi ragamar shugabancin Falasɗinawa.

Sai dai kuma yanzu ana neman komawa gidan jiya musamman daga ɓangaren Falasɗinawa. A hannu guda Robert Malley yayi ƙorafin cewa a tsawon shekaru 16 da ake ta shawarwarin sulhu akwai muhimman batutuwa da suka kamata waɗanda baá taɓo su waɗanda kuma sune tushen rikicin da ya samo asali tun shekarar 1948." Rikicin Israila da Falasɗinawa ya wuce batun yadda zaa raba wace daira ce zaá baiwa Israila, ko wani yanki ne zaá baiwa Falasɗinawa ko kuma batun yan gudun hijira da birnin Ƙudus da sauransu, akwai matsala wadda ta shafi tunanin jamaár da yanayin rayuwarsu, inda Israila ke ganin cewa Falasɗinawa basu amince da yantacciyar ƙasar Yahudawa ba wanda suka gada tun kaka da kakanni, yayin da a ɓangaren Falasɗinawa kuma suke cewa dukkan waɗannan shawarwari ana yi ne domin kakkabe haƙƙinsu da kuma yancin da suke da shi.