1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin inganta tsaro a Najeriya

December 5, 2013

Mahukuntan ƙasar sun ɗauki sabbin matakai na daidaita tsaro a daidai lokacin da wata tawagar Amirka ta isa don taimakawa wajen gano hanyoyyin cimma buƙatun cigaba a ƙasar

https://p.dw.com/p/1ATsA
Nigeria Terror Leiter der Terrorgruppe Boko Haram Sektenführer Imam Abubakar Shekau
Hoto: AP

Ƙasar Amurka ta miƙa tayin taimakawa gwamnattin Najeriya wajen yaƙi da ƙungiyar Jama'atu Ahlus Sunnah Lid Da'awati Wal Jihad da akafi sani da Boko Haram. Wannan tayi dai yana zuwa ne a dai dai lokacin da rundunar sojin ƙasar ke sauya taku game da yaƙin da take da 'yan kungiyar, ta hanyar dawo da layukan wayoyin salula a yankunan jihar Borno, bayan da al'ummar yankin suka shafe watanni ba tare da yin waya ba, da kuma gurfanar da mutane kusan ɗari biyar da ake zargi da alaƙa da Boko Haram.

A wani abun dake zaman alamu na sauya kiɗa da rawa a cikin yaƙin ta'addancin tarrayar Najeriya, ƙasar na cigaba da ɗaukar jerin sabbabin matakai na tinkarar yaƙin dake cikin shekarar sa ta huɗu da kuma ke neman gagarar ƙarfi irin na sojan kasar.

Duk da cewar dai sun kalli harin da babu irin sa cikin tsawon kusan shekaru huɗu na gwagwarmayar, ƙasa ba ta kai ga gwiwar jami'an tsaron tarrayar Najeriya da yanzu haka ke ɗaukar jeri na matakai da nufin sauyi na salo a cikin yakin.

General Ibrahim Attahiru
General Ibrahim Attahiru, mai magana da yawun dakarun sojin NajeriyaHoto: DW/Katrin Gänsler

Na farkon fari dai na zaman sake layin na waya ta salula ga ɗaukacin birnin Maiduguri da kewayen birnin da ya share wata da wattani cikin duhun sadarwar ya kuma fuskanci ƙunci dama rashi iri-iri.

Gurfanar da waɗanda ake zargi 'yan Boko Haram a Kotu

Ko bayan nan dai kuma sojan ƙasar sun ce suna shirin kaiwa kotu aƙalla ɗari biyar na 'ya'ya na ƙungiyar ta Boko Haram rundunar tsaron ƙasar dai ta ce a cikin kusan mutane 1400 da ta tantance a cikin kammamu tana shirin sakin kusan 167, a yayin kuma da ragowar 614 zasu cigaba da fuskantar jeri na tambayoyi da nufin samun ƙari na bayanai a bisa yakin.

Sabbabin matakan dai na nuna alamar sassautawa a ɓangaren sojojin da a baya suka kai ga jerin ƙunci amma kuma suka ƙare tare da ƙaruwar yawa dama ta'azzarar hari daga ƙungiyar.

A baya dai gwamnatin ta sha suka daga jeri na ƙungiyoyi ciki da ma wajen ƙasar dake zargin ta da wuce makaɗi da rawa dama aiyyana yaki kan ɗaukacin al'ummar yankin na Arewa maso gabas.

To sai dai kuma a faɗar Dr Hussaini Tukur Hassan dake zaman wani masani na siyasa da zamantakewa sabbabi na matakan na nuna alamar fara aiwatar da rahoton kwamitin da gwamantin ƙasar ta naɗa don sulhu a yankin, kwamitin kuma da ya kai ga fitar da jeri na matakai

Tawagar da Amirka ta tura Najeriya

To koma menen tasiri na jeri na matakan da gwamantin ƙasar ke ɗauka da nufin tabbatar da sauyi a cikin yanayin yankin dai, daga dukkan alamu ƙara ta'azarar rikicin da ya kai har ga ƙona jiragen yaƙin ƙasar guda biyar a farkon wannan mako dai na ɗaukar hankalin ƙasa da ƙasar da suke ƙara nuna alamun taimakawa ƙasar ta kowace fuska.

Na baya-baya dai na zaman ƙasar Amurka da wasu manyan jami'an tsaro da siyasar ta biyu suka ziyarci fadar gwamnatin kasar ta Abuja suka kuma bada tabbaci na agaji ga jami'an tsaron kasar.

Nigeria - Boko Haram Amnestie Kommission
Kwamitin sassanta tsakanin gwamnati da Boko HaramHoto: DW/A. Ubale Musa

Linda Thomas Greenfield dai na zaman muƙaddashiyar sakataren harkokin wajen Amurka dake kula da nahiyar Africa, kuma a faɗar ta sun iso Abuja ne da nufin jin dalla-dalla na irin taimakon da ƙasar ke buƙata a cikin wannan yaki.

“Muna aiki ta hadin gwiwa don taimakawa shawo kan matsalar rashin tsaro a arewacin Najeriya da kuma buƙatu na cigaban al'ummar da ake ta'alakawa da zama ummul' abai'sin matsalar. Kuma ina jin mun muna jin mun samu ganawa mai kyau. Mun yi musayar ra'ayi ,mun kuma tattauna kan batutun da shugabannin da mataimakan shugabannin kasashen biyu suka tattauna kai, dama taron na hukumar hadin gwiwar kasashen mu biyu da aka gudanar cikin watan augustan da ya wuce”.

Ko bayan batu na musanya ga bayanai dai ana kuma yiwuwar amfani da fasaha ta zamani da nufin taimakawa zaƙulo masu ta'addan da kasar ta Najeriya ta ce suna hari tare da arcewa ya zuwa makwabta na iyaka.

Mawallafi: Ubale Musa

Edita: Pinaɗo Abdu Waba