1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin tabbatar da haɗin kan ƙasa a Libiya

August 26, 2013

Libiya na fama da matsalolin tsaro da rashin daidaito, a dalilin haka ne ma ta ƙaddamar da tattaunawar samar da sulhu domin maido zaman lafiya a ƙasar

https://p.dw.com/p/19WEB
Libyan Prime Minister Ali Zeidan gives a press briefing on the Libyan Security situation on April 8, 2013 in Tripoli. Gunmen posing as security personnel kidnapped a top aide of Libyan Prime Minister Ali Zeidan, just hours after the premier revealed members of his government had received death threats, a cabinet source told AFP. AFP PHOTO/MAHMUD TURKIA (Photo credit should read MAHMUD TURKIA/AFP/Getty Images)
Ali Zeidan, Firaminintan LibiyaHoto: AFP/Getty Images

Firaministan Libiya Ali Zaidan ya ce gwamnatin ƙasar ta ƙaddamar da tattaunawa tsakanin yan ƙasa, domin yin nazarin batutuwan da suka haɗa da samar da sulhu da kwance ɗammarar 'yan tawaye. Wannan yunƙuri na zuwa ne a daidai lokacin da Libiyan ke fama da matsalar tsaro da rashin daidaito.

A 'yan watannin baya-bayan nan ma, Libiyan ta yi fama da hare-hare kan sojoji da 'yan sanda a yankin gabashin ƙasar, da ma wasu hare-haren a yankunan da ke da arziƙin man fetur, waɗanda ke zaman mafi muni tun bayan tashe-tashen hankulan da suka afku a shekarar 2011 lokacin rikicin da ya kifar da mulkin tsohon shugaba Mu'ammar Gaddafi.

Zaidan ya ce a ƙarshen tattaunawar, za a samar da kwamiti, wanda zai ƙunshi mutane daga sassa daban-daban na al'umma musamman ƙungioyoyin fararen hula, waɗanda zasu jagoranci mahawarori kan batutuwan da suka shafi makomar kundin tsarin mulkin ƙasar, da haɗin kan 'yan ƙasa da matsalar tsaro da kuma makomar waɗanda yaƙin ya ɗaidaita. Haka nan kuma ya yi alƙawarin cewa kwamitin zai yi aiki ba tare da tare da gwamnati ko majalisar ƙolin ƙasar ta sanya baki ba.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Mohammad Nasiru Awal