1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin tabbatar da zaman lafiya a Nijar

November 7, 2012

Tshofin yan tawaye da gwamnati na ƙoƙarin cire nakiyoyin da aka ɗana a yankin arewacin ƙasar a lokacin yaki ƙungiyar abzinawa ta MJN

https://p.dw.com/p/16eMw
Wüste auf dem Vormarsch ausgedörrte Landschaft auf der Fahrt nach Yatakala und Kokorou, Niger, Region Téra Wer hat das Bild gemacht?: alle Jantje Hannover Wann wurde das Bild gemacht?: alle 25.4. - 29.4.2012
Wüste auf dem VormarschHoto: DW/J.Hannover

Yaƙin tawaye da ma iskar da kamfanoni ke saki a jihar Agadez ya gurbatar da yanayi, wanda a yau al'umma ke kokowa da shi a arewacin Nijar inda wasu wuraren noma su ka gurɓace , da ma wasu rijiyoyi na shan ruwa .

Yaƙin tawaye da a kayi a arewacin Niger , ya tafi ya bar baya da ƙura , inda a yau ya tsunduma al'umma da dama da ke rayuwa a wuraren da a ka gwabza faɗa tsakanin yan tawaye da sojoji cikin matsanan ciyar rayuwa , inda gubar da a ka saki a lokacin yaƙin ta gurbatar da yananyi , ka ɗauka tun daga wuraren noma , kiwo da ma wasu rijiyoyi wanda a yanzu haka ba a anfani da ruwan.

Guɓa ta gurɓata hanyoyi da dazzuzuka

A yanzu haka idan ka ɗauki hanya daga Agadez zuwa Arlit za ka ga wata guba zubde wanda motocin kamfanoni ke zubarwa a hanya , wada a ke cema soufre , kuma ita wanan gubar duk inda ta zuba , wurin ba shi ƙara anfani , to sai dai ma,aikatar gandun daji kan yi wasu ayyuka don ceton muhalin da ya gurbace kamar yadda laftanan Mahdi jami,in gandun daji a Agadez ya shaida mana .Shi kuma Ahmed MohaMmed mazauni garin Tabelot , yankin da shi ma ya fuskanci matsala ta yakin tawaye cewa ya yi bayan gurbatar gonakan su da ma wurare na kiwo , babbar matsala a yau wada su ke fuskanta ita ce ta yadda mata ke samun matsala wajen haifuwa

###Achtung, nicht für CMS-Flash-Galerien verwenden### Grand Erg ist ein Dünenmeer, das man durchfahren muss, um in der südlichen Sahara in der Republik Niger von Bilma nach Agadez zu kommen. Aufgenommen im Jahr 2006. Foto: Desiree von Trotha
Dajin Sahara na Nijar inda galibi aka bune guba da nakiyoyiHoto: picture-alliance / Picture-Alliance

Yankin Arewacin Nijar na sake farfaɗo wa da sannu a hankali

Jihar Agadez dai , ƙasar Nijar na ƙunshe da kamfanoni da dama waɗanda su ke sakin iska mai guba da ke gurbata yanayi da ma cutar da al'umma ,sai dai ƙungiyoyin fara fula na iya nasu kokari don ganin bayan mastala kuma da sannu a hankali jihar ta fara murmurwa daga wahalolin da ta yi fama da su, sai da jama'ar yanki na ƙara neman Gwamnati da ma ƙungiyoyin duniya , da su ƙara ƙaimi wajen taimaka musu a fanin tsabtace muhali , dama kewaye don ci gaba da aiwatar da rayuwar su .

Niger Agadez Freitagsgebet
Birnin AgadezHoto: picture-alliance/ dpa

Mawallafiya :Tila Amadou
Edita : Abdourahamane Hassane