1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin ballewar yankin Kamaru ya mamaye jaridun Jamus

Mohammad Nasiru Awal RGB
October 6, 2017

Yunkurin neman ballewar yankin Kamaru mai magana da Turancin Ingilishi na daga cikin manyan batutuwan Afirka da jaridun Jamus suka mayar da hankali a kai a wannan mako.

https://p.dw.com/p/2lOoX
Nigeria Demonstration 8. Februar 2015
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Kouam

Da farko jaridar Die Tageszeitung  a labarin da ta buga mai taken wani yanki na Kamaru na son ya balle amma gwamnati na nuna halin ba sani ba sabo, jaridar ta ci gaba da sharhi inda ta ce a daya ga watan Oktoba ya kasance  rana mai muhimmanci a tarihin Kamaru, domin a ranar ce a shekarar 1961 yankin Kudancin Kamaru da ya kasance karkashin mulkin mallakar Birtaniya a hade da Janhuriyar Kamaru, wadda a 1960 ta samu 'yancin daga kasar Faransa. A bana masu fafatuka a yankin na Kudancin Kamaru sun so su yi amfani da ranar daya ga watan Oktoba don shailar 'yancin kan wannan yanki don raba gari da gwamnatin mulkin kama karya ta Shugaba Paul Biya wanda tun a 1982 ya ke jan ragamar mulki. Yankin dai na zargin gwamnatin Kamaru da mayar da su saniyar ware a kusan dukkan batutuwa da suka shafi raya kasa da samar da ababan more rayuwa ga al'umma. Gwamnatin Kamaru ba ta yi wata-wata ba wajen tura dakaru da suka yi amfani da karfi wajen murkushe wannan yunkuri, inda aka samu mace-mace. Tun wasu watanni da suka wuce yankin ke fuskantar yaje-yajen aiki da rigingimu da kame-kame da kuma kashe-kashe.

Kamerun - Proteste
An zargi 'yan sanda da laifin anfani da karfi kan jama'a masu boreHoto: Reuters/TV

Ita ma jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi tsokaci a kan rikicin tana mai cewa rikicin yankin Kudancin Kamaru mai magana da Turancin Ingilishi da ake shafe watanni ana yi ya yi muni a karshen mako, sai dai ana dora laifin kazancewar rikicin kan gwamnatin Shugaba Paul Biya, wanda tun a farkon shekara ya yi ta ba da umarnin toshe hanyoyin sadarwa na intanet gaba daya a yankin na masu magana da harshen Ingilishi. A baya nan kuma ya kafa dokar hana fita da hana gangami a yankin musamman a biranen Bamenda da Buea, inda dubban mutane suka fita zanga-zanga a karshen mako.

Kamerun Proteste
Mutane fiye da 10 sun rasa rayukansu a rikicinHoto: Reuters/TV

Bayan 'yan siyasa sun rura wutar rikici yanzu jami'a ce ke konewa inji jaridar Die Tageszeitung a labarin da ta buga game da mummunar arangama da aka yi a jami'ar birnin Nairobi, lamarin da ya sa a dole aka rufe jami'ar har zuwa wani lokaci da ba a kayade ba. Jaridar ta ce arangamar tsakanin daliban jami'ar da 'yan sanda ta samo asali ne sakamakon raunin da 'yan sanda suka yi wa wasu dalibai da dama a makon da ya gabata lokacin da suke zanga-zangar nuna adawa da kame wani dan siyasa. Ta ce wannan na zuwa daidai lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da sabon zaben shugaban kasa a Kenya mai cike da takaddama a karshen watan nan na Oktoba. Yanzu haka dai an shiga wani yanayi na rudu a fagen siyasar inji jaridar ta Die Tageszeitung.