1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin duniya na kara sojoji a Bangui

April 10, 2014

Kwamitin sulhu na Majalisar dinkin Duniya na shirin kada kuri'a domin amincewa da kudirin tura karin sojoji a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya da ke fama da rikicin addini.

https://p.dw.com/p/1Bes9
Hoto: Getty Images

Ana sa ran cewar mambobin kwamitin sulu guda 15 za su amince da tura da karin sojojin kasa da kasa har dubu 12 a watan Satumba domin shiga tsakanin musulmi da kiristocin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da ke gaba da juna.

Wannan na zuwa ne a daidai loakcin da 'yan sandan kasar suka bayyana cewar an kashe mutane kimanin talatin tare da jikkata wasu da dama a gari Dekao, yayin wani fada tsakanin sassa kasar biyu da ba sa ga majiji da juna. Jami'an gwamnati suka ce mayakan sa kai na Kungiyar Kristoci ta Anti-Balaka ne suka kai wa da 'yan kungiyar Seleka ta musulmi harin. Sai dai akasarin wadanda harin ya ritsa da su fararen hula ne.

Dakarun kiyaye zaman lafiya na Faransa sun tsaurara matakan tsaro a Bangui inda suka zafafa sintiri da nufin kawar da tashin-tashina na ramuwar gayya. Tun dai bayan da kungiyar tawaye ta Seleka ta kwace mulki tare da dora musulmi a kan karaga ne Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta fada cikin rikici na addini.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Mohammad Nasiru awal