1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin kawar da rufa-rufa a harkar aikin gwamnatin Najeriya

March 14, 2013

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da dokar da zata tilastawa shugaban Najeriya ya rinka yiwa al'ummar kasa jawabi akalla sau daya a kowace shekara.

https://p.dw.com/p/17xXi
national assembly.jpg
Hoto: DW

A kokarinta na kawar da rufa-rufa a harkar aikin gwamnati a kasar, Majalisar Datawan Najeriya ta amince da dokar da zata tilastawa shugaban Najeriya ya rinka yiwa al'ummar kasa jawabi sau daya a kowace shekara, to ko wannan ka iya tasiri a kokarin da ake na kawar da cin hanci da rashawa da ma cuku-cuku a harakar gudanar da mulki a kasar?

Bullo da wannan kudurin doka da ya baiwa 'yan Majalisar Damar tilastawa shugaban Najeriya ya yiwa al'ummar kasar jawabi a kan halin da kasa ke ciki da suka hada da batutuwan da suka shafi tattalin arziki, tsaro da ma dai halin da daukacin kasar ke ciki.

'Yan majalisar sun nuna farin ciki da samun kaiwa ga amincewa da kudurin dokar a wannan lokaci bayan jan kafar da aka fuskanta a shekarun baya. Sanin cewar manufar dokar ce ta taimaka a fannin yaki da cin hanci da rashawa da ma kamanta gaskiya a mulki ya sanya tambayar ko dokar zata yi tasiri, bisa la'akari da cewa masharahanta kan yi korafin cewa matsalar Najeriya ba rashin dokoki bane? Malam Yunusa Zakari Ya'u, jigo ne a kungiyar masu fafutukar ganin an kamanta adalci a mulki.

‘'Kowa ya sani cewar ita demokradiyya ba a yinta a cikin duhu, dole ne a kasa a kan tebur kowa ya gani, ya san ta yaya aka kasa kuma me yasa aka kasa shi haka, don me za'a zabi wannan hanya ba waccan ba! Don haka wannan doka ce wadda zata yi tasiri zata rage boye-boyen da ake fuskanta a aikin gwamnati. Fatanmu shi shugaba ya sanya hannu a kanta, kuma za'a kaita har kasa zuwa matakin jihohin da kananan hukumomi''.

Titel: DW_Nigeria_Integration2 Schlagworte: Nigeria, Präsident, Goodluck Jonathan Fotograf: Katrin Gänsler Aufnahmedatum: 04. April 2011 Aufnahmeort: Abuja, Nigeria Bildbeschreibung: Präsident Goodluck Jonathan
Hoto: Katrin Gänsler

Duk da cewa ana hangen kaiwa ga samun wannan doka a matsayin muhimmin ci gaba da zai baiwa al'ummar Najeriya sanin halin da kasarsu ke ciki ta jawabin da shugaban zai yi ta majalisun dokokin Najeriya, to sai dai ga Dr Sadeeq Abba masani a kan kimiyar siyasa da ke jami'ar Abuja na ganin akwai bukatar sake lale a kan yadda 'yan majalisar ke kalon wannan lamari.

‘'Ni a cikin fahimtata shine talakan Najeriya da matsalolin da yake ciki yafi karfin a ce wai 'yan majalisa su yi doka a tilastawa shugaban kasa ya fita kowace shekara ya yiwa al'ummar kasa jawabi. To jawabi a kan me? Babban abin tambaya kenan ya bayyana cewa tattalin arziki ya gyaru? Wanda ba zamu iya mu gani a kasa ba, ko kuwa ya yi mana jawabi kan cewar akwai tsaro, ko kuma ya gaya man cewa Najeriya ta je gaba? Duk jawaban da ake yi dinan akwai inda jawabi ya amfani talaka? Maganar da za'a yi kenan''.

Tsarin shugaba ya yiwa al'ummar kasa jawabi a kan halin da kasarsu ke ciki dai ana kalonsa a matsayin kwaikwayo ne 'yan majalisar suka yi daga wasu kasashen da suka ci gaba da ke zama linzami da ake amfani da shi wajen sanya idanu da ma tsawatawa shugabanin don kar su wuce iyaka.

Büro der Oppositionspartei "Actopm Congress of Nigeria" in Abuja, Address No. 16, Bissau Street, Wuse Zone 6, Abuja *** Bild von DW-Mitarbeiter Ubale Musa, 28. Januar 2013
Hoto: DW/U. Musa

An wa wannan doka kallon wacce zata kara karfi ga dokar 'yancin samun bayanai ga al'ummar Najeriya wacce ta baiwa 'yan kasar izinin tilastawa jami'ai da ma hukumomi su basu bayanin da suke bukata a kan yadda suke tafiyar da aiyukan da aka basu amana. Tun dai a zamanin Majalisa ta shida ne aka fara muhawara a kan wannan kudurin doka da sai a yanzu ta samun kaiwa ga wannan matsayi. Abin jira a gai shine ko wannan zai yi tasiri ga rayuwar talakan Najeriya a game da bayyana mashi gaskiyar lamurra a kasa.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idriss.
Edita: Yahouza Sadissou Madobi