1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bautar da yara a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Yusuf BalaMay 5, 2015

Kasar dai ta jamhuriyar Afrika ta tsakiya na zama waje mafi muni da dan Adam zai tsinci kansa a matsayin karamin yaro.

https://p.dw.com/p/1FKZO
Zentralafrikanische Republik Kindersoldaten Symbolbild
Hoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

'Yan tawaye masu dauke da makamai a jamhuriyar Afrika ta Tsakiya sun bayyana a ranar Talatan nan cewa zasu sako kananan yara da aka tilasta musu shiga aikin soji da sauran yaran da aka kame ana bautar da su, a wani abu da ke nuna alamun nasara ga shirin Majalisar Dinkin Duniya da ke kokarin ganin an samar da sulhu a tsakanin bangarori biyu masu gaba da juna.

Yarjejeniyar da bangarorin sojojin tawaye takwas suka rattabawa hannu za ta kai ga sakin kananan yara kimanin 6,000 zuwa 10,000 kamar yadda wata kididdiga ta asusun tallafin kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta nunar. Har ila yau 'yan tawayen sun yi alkawarin tsaida daukar sabbin yara cikin aikin na soji.

Wannan yarjejeniya kuma na zuwa bayan fara zaman samar da sulhu da zai dauki tsawon mako guda da aka fara daga ranar Litinin din nan, wanda ya kudiri aniyar kawo karshen kisan dubban mutane da sanya sama da miliyan guda kaurace wa muhallansu.

A kasar ta jamhuriyar Afrika ta tsakiya da ke zama waje mafi muni da dan Adam zai tsinci kansa a matsayin karamin yaro, a cewar Mohamed Malick Fall jami'in asusun na UNICEF wannan matsaya da aka cimma babban ci gaba ne a kokarin da asusun ke yi na ganin karshen bautar da yara.