1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin samun tsagaita wuta a Ukraine

Usman Shehu UsmanSeptember 15, 2016

Ministocin harkokin wajen Jamus da Faransa sun kai ziyara a kasar don farfado da shirin tsagaiata wuta da aka cimma tun bara amma fada ya ci gaba tsakanin gwamnati da 'yan awaren gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/1K2r5
Ukraine Kiew Treffen Steinmeier Poroschenko Ayrault
Hoto: picture-alliance/dpa/G. Savilov

Jean-Marc Ayrault da ke zama ministan harkokin wajen Faransa da takwaransa Frank-Walter Steinmeier na Jamus tare da shugaban kasar ta Ukraine Petro Poroshenko, za su duba yadda za su farfado da shirin tsagaita wutan. Kazalika za su duba yadda za'a kai ga kammala wasu tsare-tsaren siyasa da aka cimma a yarjejeniyar ta Minsk. A bangarensu 'yan aware tun a ranar Talata, suka sanar da tsagaita wuta. Haka kuma ministan harkokin wajen Jamus ya ce ita gwamnatin Ukraine ta yi alkawarin fara aiki da tsagaita wutar tun a tsakiyar daren jiya Laraba.