1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan majalisa na neman kawar da shugaban Madagaska

Suleiman BabayoMay 27, 2015

Shugaba Hery Rajaonarimampianina ya kalubalanci majalisar kasar da ta tsige shi daga kan madafun iko, bayan kada kuri'ar hakan a wannan Talatar.

https://p.dw.com/p/1FX9X
Amtseinführung Madagaskar Hery Rajaonarimampianina
Hoto: picture alliance/ZUMA Press

Majalisar dokokin Madagaskan ta kada kuri'ar ne bisa zargin shugaban da jefa addini cikin siyasa da rashin tabuka komai kan cika alkawarin da ya dauka lokacin yakin neman zabe.

A wannan Talata da ta gabata 'yan majalisa 121 daga cikin 151 suka kada kuri'a sannan suka garzaya zuwa kotun tsarin mulki domin tabbatar da kawar da Shugaban abin da zai iya jefa kasar cikin sabon rudanin siyasa. A cikin jawabi ta kafofin yada labarai Shugaba Rajaonarimampianina ya ce kasar ta Madagaska tana bukatar kwanciyar hankali. Shugaban ya ki amincewa da bai wa 'yan majalisa kyautuka kamar yadda aka saba, kamar manyan motocin alfarma da wasu abubuwa.

A zaben shekara ta 2013 aka zabi Shugaba Hery Rajaonarimampianina, abin da ke zama zabe na farko tun bayan juyin mulkin shekara ta 2009, a kasar ta Madagaska mai yawan mutane kimanin milyan 23.