1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen Majalisar Dokoki a jihar NRW

May 9, 2010

Zaɓen Majalisar Dokoki a jihar Northrhine Westfalia ya kawo canjin gwamnati

https://p.dw.com/p/NJuz
Pirimiyan jihar Northrhine Westfalia, Jürgen RüttgersHoto: AP

Tun kafin zaben na majalisar dokokin jihar Northrhine Westfalia a ranar Lahadi, aka ga alamun cewar masu kada kuri'u  zasu nuna  rashin goyon bayan su ga aiyukan  da gwmanatin da  tayi mulki har ya zuwa  wannan lokaci, wato karkashin Pirimiya Jürgen Rüttgers na jam'iyar CDU da Pinkwart na jam'iyar  FDP. Sakamakon da aka samu daga zaben ya nunar da cewar masu zabe sun  kada kuri'ar rashin goyon baya ga wannan gwamnati, inda jam'iya mafi girma a wannan hadin gwiwa, wato CDU, tayi asarar akalla kashi goma da rabi cikin dari na kuri'u, idan aka kwatanta da shekaru hudu da suka wuce. A  zaben na jranar Lahadi,  jam'iyar ta CDU ta sami abin da bai wuce kashi talatin da  hudu da digo hudu cikin dari ba, idan aka kwatanta da misalin kashi arba'in da digo shidda da ta samu shekaru hudu da suka wuce. Dangane da haka,  Pirimiyan jihar ta Northrhine Werstfalia,  kuma shugaban jam'iyar CDU a jihar,  Jürgen Rüttgers  yace ya  dauki  alhakin duk irin kayen da jam'iyar tasha a  zaben na jihar Northrhine Westfalia.

Yace wannan   zabe  na yau   ya zama mummunan abu ga jihar  Northrhine Westfalia  da kuma gareni musamman. Sakamakon da aka samu  ya zama na bakin ciki , musamman saboda mun gudanar da kampe ne tare da imanin cewar mun gudanar da kyakkyawan aiki tsawon shekaru biyar na mulkin mu ga al'ummar   jihar Northrhine Westfalia.

Zaben majalisar dokoki a wannan jiha, da ita ce tafi yawan jama'a a   tsakanin jihohi goma sha shida na Jamus baki daya, ya dauki hankali, musmman ganin cewar  sakamakon da aka samu, zai zama mai muhimanci ga tsarin aiyukan mulki a kasa baki daya, musamman  a gwmnatin taraiya da aiyukan ta a babbar majalisar dokoki ta Bundesrat. Shugaban jam'iyar  adawa ta Social Democrats  wato SPD a majalisar  dokoki ta jihar, Hannelore Kraft dake jawabi gaban dimbin magoya bayan ta, tace:

Yanzu dai ya tabbata masu zabe sun kawar da gwamnatin hadin gwiwa ta CDU da FDP. Sakon da muke dauke dashi daga jihar Northrhine Westfalia shine: yanzu dai jam'iyar SPD, ta farfado inda aka santa a da.

To sai dai kuma  ko da shike jam'iyun CDU da FDP  ba zasu sami damar ci gabada aiyukan mulki na  jihar ta Northrhine Westfalia bayan zaben na ranar Lahadi ba, amma har yanzu tana kasa tana dabo a game da    yadda za'a tafiyar da mulkin jihar zuwa gaba.  Jam'iyar Greens ta masu  da'awar kare muhalli ta sami abinda ya kai kashi  goma sha  biyu da digo ukku,  wanda koda ta hada  kai da jam'iyar SPD ba zata sami  cikakken rinjaye a majalisar ba. Duk  da haka,  shugaban  jam'iyar ta Greens, Sylvia Lohmann tace:

Yamacin na yau  babu shakka zai kasance   mai tsawo, kuma ba kamary adda  wasu suke nunarwa ba, wnanan yamaci ba zai zama na bakinc iki a garemu ba, a daura dfa haka ma,   wanan yaymmaci na farin  ciki ne a garemu,  saboda nasarorin da muka samu.

Shugaban jam'iyar SPD na kasa baki daya, Sigmar Gabriel ya baiyana farin cikin sa ga sakamakon zaben na jihar Northrhine Werstfalia,, inda yace ranar ta Lahadi, kyakkyawar rana ce ga wannan jiha.

                  Mawallafi: Umaru Aliyu

                  Edita: Yahouza Sadissou