1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaɓen 'yan majalisun dokokin Italiya.

February 22, 2013

Jam'iyyun siyasa sama da guda biyar zasu fafata, a cikin zaɓen na lahadi da zai zama wata ƙarawa tsakanin jam'iyyun siyasa masu ra'ayin yan mazan jiya da kuma masu ra'ayin sauyi.

https://p.dw.com/p/17kDs
Italian Premier Mario Monti poses next to the logo of his new party in Rome, Friday, Jan. 4, 2013. Mario Monti is moving forward in his campaign, unveiling his logo for February elections and pledging to scrutinize parliamentary candidates on his ticket to eliminate those with conflicts of interest, convictions or organized crime ties. Monti summoned journalists Friday evening to show off his symbol, a circle with stripes in red, white and green, the colors of the Italian flag, and the slogan "Civic choice with Monti for Italy." (Foto:Riccardo De Luca/AP/dapd)
Hoto: AP

Mutumin da ke zaman bazata a cikin wannan zaɓe na yan' majalisun dokoki shi ne wani tsohon ɗan wasanin ban dariya Beppe Grillo wanda ke shugabantar wata jam'iyyar da a ke kira da sunan mai tarmamu biyar.Wanda da alama zai iya dama lisafi ga haɗin gwiwar jam'iyyun siyasa masu neman sauyi da aka daɗe ana tsamani su ne zasu sami nasara a zaɓen.

Jam'iyyun siyasar da ake tsamani zasu taka rawa a zaɓen

A hasashe na ƙarshe da aka yi a ƙasar ta Italiya kafin zaɓen ya nuna cewar jam'iyyar yan gurguzu ta Pier Luigi Bersani ita ce za ta zo ta farko,yayin da jam'iyyar Mouvement 5 Etoile ta tsohon ɗan wasannin ban dariyar za ta zo ta uku,bayan jam'iyyar Silivio Berlusconi ta biyu ,sai Mario Monti fitaccen shugaban gwamnati.

Pier Luigi Bersani, head of the main left-wing opposition Democratic Party (PD), addresses delegates during a PD party meeting in Rome on February 4, 2011. 'Berlusconi needs to resign,' said Bersani accusing the Italy's prime minister of deceiving voters over fiscal reforms included in the federalism law. Italian President Giorgio Napolitano rejected a government decree granting greater taxation powers to city administrations in a major blow for Prime Minister Silvio Berlusconi. AFP PHOTO / ANDREAS SOLARO (Photo credit should read ANDREAS SOLARO/AFP/Getty Images)
Pier Luigi Bersani jagoran jam'iyyar masu ra'ayin sauyiHoto: ANDREAS SOLARO/AFP/Getty Images

Ƙasar Italiya wacce ita ce ke da ƙarfin tattalin arziki na uku a nahiyar Turai ta sami kan ta a cikin wani hali na tsaka mai wuya tun a tsakiyar shekara 2011. Saboda tsauraran matakan da gwamnatin Mario Monti ta ɗauka na ƙara kuɗaɗen haraji da rage yawan ma'aikata da kuɗaɗen fansho.Abin da ake gani zai sa faduwar fitaccen shugaban gwamnatin amma ya ɗaukaka Grillo.Ga ma abin da ya ke faɗa dangane da jam'iyyarsa.Ya ce ''Wannan yunƙuri na mu ;sa'ida ce ga yara mu da bayan mu,domin ceto ƙasar mu daga irin wahalolin da ta shiga na bashi da Monti ya karɓo. Ya ce mu ,muna son mu daidaita tafiya zuwa ritaya daga shekaru 70 zuwa 60''.

Tsohon shugaban gwamnatin ya koma yin siyasa

Silvio Berlusconi mutumin da a ke yi wa kallon wanda ya yi mutuwar siyasa kuma ya farfaɗo wanda aka tilasawa yin marabus a cikin watan Nuwanba na shekara ta 2011; domin ba da matsayin ga Mario Monti. Ya kwashe dogon lokacin kafin ya baiyana cewar zai yi takara duk da ma cewar ya na da shekaru 76 da haifuwa. Ana gani cewar har yanzu ya na da ta faɗi a fagen siyasar ƙasar, domin kuwa ya mallaki kafofin yaɗa labarai da suka haɗa da telbijan wanda kuma a baya baya nan, ya daɗa baiyana a kafofin tare da yin ƙorafin cewar zai ramkawa jama'a kuɗaɗen haraji da wanda ya gaje shi ya zabatare musu.Ya ce ''sabuwar gwamnatin mu da za ta zo idan mun sami nasara za ta soke tsauraran dokoki da aka ɗauka, ya ce zamu soke kuɗaɗen haraji a kan gidaje sannan mu rankawa jama'a harajin da aka cire musu a shekarar bara''.

Italian former prime minister and owner of the AC Milan football team, Silvio Berlusconi, arrives at the AC Milan training grounds in Milanello on December 8 , 2012. Prime Minister Mario Monti's government hung by a thread the day before as predecessor Silvio Berlusconi prepared to return to the fray, with his supporters arguing that Italy is now far worse off than before. AFP PHOTO / GIUSEPPE CACACE (Photo credit should read GIUSEPPE CACACE/AFP/Getty Images)
Silvio BerlusconiHoto: Getty Images

A shekaru 62 da ya ke da su a duniya Pier Luigi Bersani jagoran jam'iyyar yan gurguzu tsohon ministan ci-gaba masana'antu da kamfanoni na Italiya na samun ƙwarin gwiwa a zaɓen da masu lura da al'ammuran yau da gobe ke hasashen cewar zai kasance na yin hukunci jama'ar a kan manyan yan siyasar na ƙasar wanda ake da fushin su.

Daga ƙasa za a iya saurron wannan rahoto

Mawallafi : Abdourahamane Hassane.
Edita : Zainab Mohammed Abubakar