1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a binciki miyagun laifuka a Myanmar

Yusuf Bala Nayaya
November 28, 2017

Bukatar wannan bincike na Majalisar Dinkin Duniya da kasar Bangaladash da Saudiyya suka gabatar ta samu goyon baya na kasashe mambobi 33 daga cikin 47.

https://p.dw.com/p/2oPl2
Bangladesch | Humanitäre Hilfe für Rohingya
Hoto: DW/ P. Vishwanathan

Hukumar da ke kula da harkokin kare hakkin bil Adama a Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a wannan Talata cewa za ta yi nazari kan halin da Musulmi 'yan Rohingya marasa rinjaye ke ciki a wani zama na musamman da za a yi a ranar biyar ga watan Disamba a Geneva.

Bukatar wannan zama da kasar Bangaladash da Saudiyya suka gabatar ta samu goyon baya na kasashe mambobi 33 daga cikin 47 da ke karkashin hukumar ciki har da wadannan kasashe biyu.

A cewar kamfanin dillancin labaran Reuters majiyar ta Majalisar Dinkin Duniya, rahoto da ta fitar a ranar Litinin ya nunar da cewa zaman na musamman zai karkata kan binciken aikata kisa da fyade da ma wasu aiyukan na rashin imani da aka aikata wa 'yan Rohingya, abin da ya sanya 'yan kabilar sama da 600,000 suka yi wa muhallansu kaura don neman mafaka a Bangaladash.