1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a fara gwajin maganin rigakafin Ebola

Ahmed SalisuMarch 5, 2015

Kungiyar Lafiya ta Duniya WHO ta ce za ta fara gwajin maganin rigakafin cutar nan ta Ebola ranar Asabar da ke tafe.

https://p.dw.com/p/1ElSC
Symbolbild - Ebola Virus
Hoto: picture-alliance/dpa

Shugabar WHO din Margaret Chan ta shaidawa manema labarai cewar za a gudanar da gwajin ne a kasar Gini kuma idan har aka samu nasara to maganin zai zama wani babban makami na yakar cutar.

Wannan dai shi ne karon farko da za a yi gwajin rigakafin wannan cuta kan mutane da damar gaske a kasar ta Gini wadda ke cikin kasashen nan na yammacin Afirka uku da cutar ta yi ta'adin gaske.

Hakan dai na zuwa ne daidai lokacin da kasashe suka fara samun nasara a yaki da ake da wannan cutar ta Ebola, don ko a dazu ma Liberiya ta ce an sallami mutum guda ya rage ya an dauke da kwayar cutar.