1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a sami karancin agaji a duniya

February 19, 2019

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kungiyoyin agaji na gab da kashe kudaden da ke a hannunsu, a ayyukan jin kai da suke yi a kasar Yemen.

https://p.dw.com/p/3DghZ
Syrien Hilfskonvoi in Kafr Batna
Hoto: Reuters/B. Khabieh

A wani kiyasin da ta yi, Majalisar Dinkin Duniya ta ce kudaden da kungiyoyin za su bukata don ci gaba da samar da agajin a Yemen da wasu sassa na duniya, za su kai sama da dalar Amirka biliyan hudu.

Jagoran hukumar agajin na Duniya Mark Lowcock, ya shaida wa taron kwamitin sulhu cewar batun cimma bukatun jin kai a kasashen duniyar, shi ne babban kalubalen da ke gabansu a yanzu.

A ranar 26 ga wannan watan na Fabrairu ne dai ake sa ran Sakatare Janar na Majalisar Dinkin na  Duniya, Antonio Guterres ya shirya wani taro a birnin Geneva na kasar Switzerland kan wannan bukata.