1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za´a aiwatar da canje canje a Ukraine don gudanar sabon zabe

June 2, 2007
https://p.dw.com/p/BuK1
´Yan majalisar dokokin kasar Ukraine sun amince da aiwatar da wasu canje canje da ake bukata don gudanar da zabe na gaba da wa´adi. Hakan na kunshe ne a cikin wani shiri da nufi kawo karshen gwagwarmayar neman iko tsakanin shugaban kasa mai ra´ayin kasasehn yamma Viktor Yuschcenko da FM Viktor Yanukovich mai samun daurin gindin fadar Kremlin. Shugaba Yuschchenko ya kara wa´adin da aka bawa ´yan majalisa don kafa wasu dokoki da ake bukata bisa manufar shirya zaben. Bayan tataunawar da suka yi a karshen mako shugaba Yushchenko da FM Yanukovich suka amince da shirya sabon zaben na gaba da wa´adi a ranar 30 ga watan satumba. Manazarta harkokin siyasa sun ce rashin aiwatar da canje canje ka iya janyo tashe tashen hankulan siyasa a cikin kasar.