1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za´a gudanar zaben Pakistan a ranar tara ga watan janeru

November 11, 2007
https://p.dw.com/p/CAH9

Shugaban Pakistan Pervez Musharraf ya kare matakin da ya dauka na kafa dokar ta baci. Yayin da yake magana a gun wani taron manema labarai a birnin Islamabad Musharraf ya ce ya kamata Pakistan ta shirya zaben ´yan majalisar dokoki kafin ranar 9 ga watan janerun shekara mai zuwa. Ya yi alkawarin tube kakin soji sannan a rantsad da shi a matsayin shugaban kasa farar hula da zarar kotun kolin kasar ta tabbatar da sake zabinsa.

Musharraf:

“Dokar ta baci zata tabbatar da an gudanar da zaben cikin adalci da kwanciyar hankali. Ba zamu tsoma baki a shirye shiryen zaben ba. Muna gayyatar masu sa ido daga ketare su zo su ga yadda zaben zai gudana. Duk wanda aka tsare shi an yi haka ne saboda ya karya doka. Amma ina sa ran a sako dukkannensu domin su shiga cikin zaben.”

Shugaba Musharraf ya kuma ba da sanarwa cewa za´a rushe majalisar dokoki a ranar 15 ga watannan na nuwamba to amma ba fadi lokacin da za´a dage dokar ta bacin ba.