1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Afurka ta Kudu

April 14, 2004

A yau laraba ne ake gudanar da zabe a kasar Afurka ta Kudu, kuma manazarta sun hakikance cewar jam'iyyar ANC ce zata sake cinye zaben

https://p.dw.com/p/Bvkj
Shugaba Thabo Mbeki a yakin neman zabe
Shugaba Thabo Mbeki a yakin neman zabeHoto: AP

A cikin wani rahoton da ta gabatar makon da ya gabata jaridar "Mail and Guardian" mai sassaucin ra’ayin gurguzu a kasar Afurka ta Kudu tayi nuni da kwarin guiwar dake akwai game da cewar jam’iyyar ANC ce zata sake lashe zaben kasar da ake gudanarwa karo na uku a yau laraba kuma tare da gagarumin rinjaye. Bisa ga ra’ayin Tom Lodge, masanin kimiyyar siyasa a jami’ar Witwatersrand ta birnin Johannesburg, wannan nasarar tana da nasaba da tarihi na danniya da kama karya da bakar fatar ATK suka sha fama da shi a hannun farar fatan kasar. Wadannan bakar fata ba su manta da rawar da ANC ta taka domin ‚yantar da su daga wannan kagi na bauta ba. Tom Lodge ya kara da cewar:

"ANC tayi amfani da wannan batu a yakinta na neman zabe. Shugaba Thabo Mbeki ya ziyarci kauyuka masu tarin yawa yana mai tabbatarwa da jama’a cewar mu ne jam’iyyar Nelson Mandela, mu ne jam’iyyar wannan gwarzon namiji ma’abuci dattaku. Ku tabbata cewar mu ne kadai zamu iya tanadar muku da muhimman abubuwan da kuke bukata domin kyautata makomar rayuwanku. ANC, a takaice, tana iya dogara akan kyakkyawar amannar da take da shi a zukatan jama’a. Jam’iyyar na iya tinkaho da tarihinta da kuma biyayyar da take da shi daga jama’a."

Dukkan binciken da aka gudanar domin neman ra’ayin jama’a, sun yi nuni da cewar jam’iyyar nan ta Democratic Alliance dake da angizon farar fata, duka-duka goyan bayan da zata samu ba zai zarce na kashi goma ko 12% na jumullar kuri’un da za a kada a zaben na yau laraba ba. A sakamakon haka ne, shugaban jam’iyyar Tony Leon, a yakinsa na neman zabe ya dukufa wajen janyo hankalin bakar fata zuwa ga barazanar da kasar ATK ke fuskanta game da wanzuwa karkashin wani tsarin mulki na jam’iyyar siyasa daya kwal. To sai dai kuma wannan maganar ba ta da tushe a cewar Rehana Rousov, editar jaridar ‚Business Day‘ ta ATK. Ta ce ba ta tsammanin cewar ATK zata taba komawa karkashin wani tsarin mulki na jam’iyyar siyasa daya kwal. Domin kuwa hatta a wannan zaben jam’iyyun siyasa 14 ne ke gwagwarmaya da juna. A saboda haka maganar barazanar komawa karkashin tsarin mulkin siyasa daya ba ta taso ba. Shi ma Tom Lodge, masanin kimiyyar siyasa daga jami’ar Wiwatersrand ta Johannesburg, ba ya zaton rinjaye na kashi biyu bisa uku da ANC ke da shi a tsakanin masu kada kuri’u a ATK zai fid da kasar daga kan hanya madaidaciya ta demokradiyya da take kai a yanzun. A cikin shekaru 10 da tayi tana mulki ANC ta gina gidaje kimanin miliyan daya da dubu dari shida don amfanin talakawa ‚yan rabbana ka wadata mu. Bugu da kari kuma an samu karin mutane miliyan tara dake da ikon samun ruwan sha mai tsafta da wutar lantarki a unguwannin bakar fata, duk kuwa da cewar har yau akasarin al’umar ATK suna zama ne hannu-baka-hannu-kwarya. Kimanin kashi 42% na al’umar kasar ba su da aikin yi a baya ga cutar nan ta Aids da ta zame musu kayar kifi a wuya. Mai yiwuwa a zabe na gaba wadannan matsaloli na talauci da rashin aikin yi da kuma yaduwar cutar Aids su ne zasu taka muhimmiyar rawa.