1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Rudani yayin kirga kuri'u

Abdoulaye Mamane Amadou
November 5, 2020

A Amirka an fuskanci rudani yayin kirga kuri'un zaben shugaban kasar da aka gudanar tsakanin Shugaba Donald Trump da abokin hamayyarsa Joe Biden.

https://p.dw.com/p/3kvOj
US Wahl 2020 Donald Trump
Hoto: Chris Kleponis/UPI Photo/imago images

A Amirka an samu jinkiri a yayin bayyana sakamakon wanda ya samu nasara a zaben shugaban kasa. Tun ba a yi nisa wajen kidayar kuri'un ba Shugaba Donald Trump y bayyana cewa ya lashe zaben wanda hakan ya sabawa ka'idojin tsarin dimukuradiyya, a yayin da abokin hamayyarsa Joe Biden ya bukaci magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu su jira har a bayyana wanda yayi nasara a zaben.