1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwango: Kabila ba zai tsaya takara ba

Yusuf Bala Nayaya LMJ
August 9, 2018

A watan Disamba me zuwa ne wa'adin mulkin Shugaba Joseph Kabila na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango zai kai karshe, shugaban ya bayyana cewa ba zai tsaya takara ba, shin kasar na tunkarar zaman lafiya ne ko kuwa rikici?

https://p.dw.com/p/32u5W
DRC Präsident Joseph Kabila
Shugaba Joseph Kabila na Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Reuters/K.Katombe

A karkashin kundin mulkin kasar ta Kwango dai, tun a shekarar 2016 ne wa'adin mulkin Shugaba Joseph Kabila ya kare. Sai dai rikici da rashin tabbas da kasar ta samu kanta a ciki ya hana gudanar da zaben tun a wancan lokaci. A yanzu dai ranar 23 ga watan Disambar wannan shekarar ta 2018 aka kebe don yin wannan zabe. Mai magana da yawun gwamnati Lambert Mende ya yi jawabi ga 'yan kasar, inda ya ce Emmanuel Ramazani Shadary tsohon ministan cikin gida kuma sakataren jam'iyyar PPRD ta Shugaba Kabila ne zai gaji Kabila a takarar zaben na Disamba.

Kongo Emmanuel Ramazani Shadary
Emmanuel Ramazani Shadary dan takara shugaban kasa a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango karkashin jam'iyya mai mulki ta KabilaHoto: REUTERS

Rawar da Shadry zai taka

Ana kallon Shadry a matsayin wani mara karfin fada aji haka kuma ana kallonsa a matsayin me biyayya ga Kabila kana ba shi da alaka da manyan 'yan siyasa ko sanin manyan jami'an soja wadanda ke taka rawa ga makomar mulkin kasar. Wasu masharhanta dai na ganin Kabila zai yi dabara irinta Putin-Medvedew ne, wato lokacin da shugaban Rasha ya koma firaminista saboda wa'adinsa ya cika, babban na kusa da shi ya zama shugaban kasa. Shadry shi ya dace da zama Medwedew a Kongo. Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar za ta yi nazari kan 'yan takara 20 da za su shiga zaben na watan Disamba wadanda suka hadar da mata uku da dan takara daga babbar jam'iyyar adawa Felix Tshisekedi domin ganin ko sun cancanta su bayyana a cikin sunayen da za a fitar a cewar Jean Pierre Mulumba da ke Magana da yawun hukumar zaben CENI:

Makomar takarar Bemba

Internationaler Strafgerichtshof Jean-Pierre Bemba
Jean-Pierre Bemba da kotu ta wanke daga zargin aikata laifukan yaki a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, kana dan takarar shugabancin kasarHoto: picture-alliance/AP Photo/M. Kooren

Akwai dai fargaba kan takarar Jean-Pierre Bemba wanda kotun daukaka kara ta wanke bayan zargin laifukan yaki a kotun ICC da ke a birnin The Hague na kasar Holland, wanda kuma ya koma kasar da aniya ta gabatar da bukatar neman tsayawa takarar shugabancin kasa a hukumar zabe ta CENI ko zai tsallake kuwa? Lokaci ne dai zai nuna.

Wani dan takarar shi ne Moise Katumbi wanda ma ba a ba shi dama ba ta komawa kasar dalili kuwa shi ne yana da tuhuma a gaban kuliya. 'Yan sanda na barazanar kama shi da zarar ya koma gida. Magoya bayansa a Katanga sun yi bore har ma da gwabzawa da 'yan sanda. Wasu masu sharhi kan lamuran siyasa a kasar ta Kwango dai suma na nuna fargaba kasancewar Kabila ba da dadewa ba ne ya samar da sauye-sauye a rundunar sojan kasar. Wasu matasan kasar kuwa kamar kungiyar 'yan fafutukar kare al'ummar Kwango ta LUCHA na masu ra'ayin cewa ba za ma su je zaben na watan Disamba ba, kasancewar sun yi amanna babu wani sauyi da za a samu a kasar.