1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben jihohi a Iraki

April 20, 2013

Ana ci gaba da gudanar da zaben yankuna na kasar Iraki a wannan Asabar

https://p.dw.com/p/18K0q
Hoto: Reuters

To sai dai an samu hare-hare kan rufunan zabe biyu. Fiye da mutane 100 sun hallaka cikin hare-hare da aka kai kafin zaben na yau da ke zama zakaran gwajin dafi ga zaman lafiya a kasar, bayan janyewar dakarun Amirka a karshen shekara ta 2011. Zaben na zuwa ne shekara 10 bayan kutsen da Amirka ta jagoranta, wanda ya kawar da gwamnatin Marigayi Saddam Hussein. Masu zabe kimanin miliyan 14 za su tantance 'yan majalisun lardunan kasar 18. 'Yan takara 8000 ke fafata neman kujeru 378.

Bayan kada kuri'a Firaministan kasar ta Iraki Nuri al-Maliki ya ce, duk masu tsoron makomar kasar na komawa cikin tashin hankali ko mulkin kama karya, to su sani gwagwarmayar ta koma kan akwatunan zabe.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Halima Balaraba Abbas