1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben jin ra'ayi a yankin Scotland

September 17, 2014

Ranar Alhamis, al'ummar Scotland suke kada kuri'ar baiyana ra'ayi a game da ko suna bukatar ci gaba da zama karkashin daular Britaniya.

https://p.dw.com/p/1DDxt
Schottland Referendum
Hoto: Reuters/Russell Cheyne

A kuri'ar ta ranar 18 ga watan Satumba, al'ummar yankin Scotland za a nemi su baiyana ra'ayinsu ne kawai a game da ko suna bukatar zama masu cikakken mulkin kansu. Idan har 'yan Scotland din suka nuna bukatar samun mulkin kan nasu, hakan ba yana nufin tun daga ranar Alhamis sun zama masu mulkin kansu bane. Ranar da aka ware domin cimma wannan buri ita ce ranar 24 ga watan Maris na shekara ta 2016. Akalla kafin wannan rana wajibi ne a kammala al'amura masu tarin yawa na siyasa da tattalin arziki tattare da mulkin kan. Sai dai kuma a yayin da 'yan kishin kasa na Scotland suke ci gaba da fafitikar ganin yankin ya balle daga Britaniya, 'yan siyasa a Ingila suna ci gaba da kira ga 'yan Scotland din su yi tunani mai zurfi kafin su yanke shawara. Pirayim Minista David Cameron a wani sako zuwa garesu, yace:

"Sakonmu zuwa ga mutanen Scotland shine: muna so ku ci gaba da zama da mu. Da zuciyarmu, da imaninmu, da kwakwalarmu da jikinmu, muna so ku ci gaba da zama da mu. Kada ku yi kuskuren daukar cewar muna so ku zauna damu ne na dan lokaci. Burinmu shine ku ci gaba da zama damu har abada. Ni kaina, in ni ne yau, ba ni ne gobe ba. Kada ku dauka don ina mulki a yau, wajibi ne ku fice daga taraiyar Britaniya, saboda ba zan ci gaba da zama har abada ba. Amma idan kuka fice yanzu daga Britaniya, to kuwa wannan mataki ne na har abada".

Idan har yankin na Scotland ya zabi ficewa daga Britaniya, to kua wata sabuwar kasa zata samu a Turai daga shekara ta 2016. Wannan sabuwar kasa tilas ta nemi shiga kungiyar hadin kan Turai da kungiyar tsaron Nato. A karshen wa'adin, tilas ta gabatar da takardun neman a dauke ta a kungiyar ta Nato. Hakan kuwa ba zai samu ba sai idan takatrun sun sami amincewar dukkanin wakilan Nato.

David Cameron Ansprache Referendum 15.09,2014
Pirayim Ministan Britaniya David CamronHoto: Reuters/Dylan Martinez

Kasashe da dama suna nuna damuwarsu a game da sakamakon da zi biyo bayan wannan kuri'a ta jin ra'ayi.Tun da kuwa bisa al'ada, 'yan Scotland sun fi nuna goyon baya ga manufofin Turai fiye da yan Ingila, saboda haka ballewar yankin daga Britaniya zai kara karfafa aiyukan masu kyamar nahiyar Turai a Ingila. A takaice idan yan Britaniya a shekar ta 2017 suka zo kada kuri'ar jin ra'ayi a game da wakilcin kasarsu a kunghiyar hadin kan Turai, rashin ra'ayin yan Scotland miliyan hudu, yana iya zama mai muhimmanci, yadda masu adawa da Turai din za su sami galaba. Bugu da kari kuma, kasashen na Turai suna tsoron cewar idan Scotland ta sami mulkin kanta, hakan yana iya baiwa sauran kungiyoyi masu gwagwarmayar neman yancin yankunansu, misali a Spain ko Belgium kwarin gwiwar ci gaba da neman biyan bukatunsu. Misali, nan gaba ma, yankin Ireland Ta Arewa na iya neman mulkin kansa daga Britaniya. Duk da haka, masu mulki a Scotland suna ganin wahalolin da Scotland zata fuskanta idan ta zama mai mulkin kanta ba masu dorewa bane. Shugaban gwamnatin yankin Alex Salmond tun kafin kuri'ar yana nunarwa al'ummarsa cewar Scotland ba ta bukatar Britaniya.

"Al'ummar Scotland ba zasu bari a rika tsoratar dasu ba, ta hanyar amfani da manyan kamfanonin man fetur ko manyan kantuna ko kuma katuwar gwamnati dake mulki a London. Ba zamu bari wannan gagarumar dama da ta samu ta wuce mu ba, wato damar samun karuwar jin dadin rayuwa da zamantakewa da ta dace damu".

Symbolbild Referendum Unabhängigkeit Schottland
Tutar Britaniya ce ko tutar Scotlnd za ta ci gaba da kadawa a EdinburghHoto: Andy Buchanan/AFP/Getty Images

Ya zuwa watan Maris na shekara ta 2016, Fam na Ingila zai ci gaba da zama kudin yau da kullum a Scotland, yayin da Ingila, wato Britaniyya gaba daya, tace zata ci gaba da daukar lamunin dukkanin basussukan dake kan kasar, ciki har da na bangaren Scotland.