1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben raba gardama a Kirimiya

March 16, 2014

An yini ana kada kuri'a a kan makomar yankin Kirimiya na Ukriane bayan makwani na tsakanin Rasha da kasashen Yamma. Nan da 'yan sa'o'i ake sa ran rufe rumfunan zabe.

https://p.dw.com/p/1BQYW
Simferopol Referendum Krim Ukraine Russland Konflikt Krise 2014
Hoto: Reuters

Masu kada kuri'a za su yanke hukunci kan walau ko yankin ya ci-gaba da zama wani bangaren kasar Ukraine ko kuma ya hade da kasar Rasha. Rahotanni suka ce kusan dai babu makawa masu son komawa bangaren Rasha za su yi rinjaye, kasancewa kabilar Rashawa ta na da rinjayen sama da kashi 60 cikin dari.

Kasashen Yamma da ke dasawa da Ukraine sun bayyaan zaben a matsayin haramtacce. Amma su kuwa al'ummar yankin, tuni suka fara wakokin samun 'yanci. An ruwaito cewa a yanzu haka Rasha ta tura sojoji kimanin dubu 22 a Kirimiya. A jiya Asabar ne dai su ma wasu yankunan gabashin Ukraine suka fara zanga-zangar neman ballewa daga wannan kasa, biyo byan yunkurin da jama'ar Kirimiya suka dauka na rabuwa da kasar.

Wani kudurin da kwamitin sulhu na MDD ya gabatar a ranar asabar don neman haramta zaben raba gardaman bai samu nasara ba, inda kasar Rasha ta yi amfani da kujerar na ki domin hana kudurin shiga. Kasar China ita ma ba ta kada kuriar ba a majalisar.A yau Lahadi kuwa ma'aikatar harkokin wajen China ta ba da hujjar cewa kudurin haramta abin da ke faruwa a Kirimiya zai kara ruruta rikicin ne kawai. Don haka Beijing ta bukaci a warware takaddamar bisa sulhu.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohamadou Awal Balarabe